Satar akwatin zabe: Jigon APC ya kare Buhari kan umurnin da ya bayar

Satar akwatin zabe: Jigon APC ya kare Buhari kan umurnin da ya bayar

Shugaban kungiyar kamfen din gida-gida na jamiyyar All Progressives Congress (APC), Bola Ilori ya bayyana cewa umurnin da Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ba hukumomin tsaro na su yi hukuncin ba sani-ba sabo ga wadanda suka sace akwatin zabe a lokacin zaben kasar hanya ce ta hana afkuwar hakan a lokacin zabe.

Yace furucin Shugaban kasar zai magance yawan kasha-kashe da tashin hankali a lokacin zabe sannan zai hana ayi magudi a zaben wanda a cewarsa ta zamo rowan dare a zaben Najeriya.

Ilori, wanda yayi Magana a Akure, babbar birnin jihar Ondo, yayinda yakje jagorantar rangajin APC a yankuna daban-daban na jihar domin ci gaba da kamfen din gida-gida yace APC ta shirya gudanar da zabe na gaskiya da amana a zaben gobe.

Satar akwatin zabe: Jigon APC ya kare Buhari kan umurnin da ya bayar

Satar akwatin zabe: Jigon APC ya kare Buhari kan umurnin da ya bayar
Source: Depositphotos

Jigon na APC, wanda ya kasance tsohon kwamishina a jihar Ogun yace nasarorin da gwamnatin shugaba Buhari ta samu a hukumomi daban-daban na tattalin arzikin kasar, zai bashi dammar yin nasara a zaben ranar 23 ga watan Fabrairu.

KU KARANTA KUMA: Dan majalisar APC a Benue ya sauya sheka zuwa PDP, ya bayar da hujja

A wani lamari na daban, Legit.ng ta rahoto cewa Jihar Katsina ta zarcewa dukkan jihohin Najeriya 35 da Abuja wajen yawan karban katin zabe a zaben da za'a gudanar ranan Asabar, 23 ga watan Febrairu da 9 ga Maris, 2019.

Wannan na kunshe ne cikin lissafin da hukumar gudanar da zabe ta kasa mai zaman kanta wato INEC ta saki ranan Alhamis bayan hira da manema labarai a dakin taron ICC Abuja.

Shafin NAIJ.com Hausa ne ya koma LEGIT.ng Hausa

Latsa kuga sabuwar manhajar Legit.ng Hausa a wayarku ta salula: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafukanmu na dandalin sada zumunta sune:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Online view pixel