Da duminsa: Rundunar 'yan sanda ta cafke Sanata Rafiu Ibrahim ana gobe zabe

Da duminsa: Rundunar 'yan sanda ta cafke Sanata Rafiu Ibrahim ana gobe zabe

- Rundunar 'yan sanda ta cafke Sanata Rafiu Ibrahi, mai wakiltar mazabar Kwara ta Kudu da ke jihar Kwara, karkashin jam'iyyar PDP

- Rundunar ta cafke Sanata Ibrahim, wanda ke neman tazarce, ana gobe zaben shugaban kasa da 'yan majalisun tarayya

- Rahotanni sun bayyana cewa APC ce ta bukaci rundunar 'yan sanda ta cafke Sanatan biyo bayan wani rikici da ya barke a garin Ojuku da ke mazabarsa

Rahoton da legit.ng Hausa ke samu yanzu na nuni da cewa rundunar 'yan sanda ta cafke Sanata Rafiu Ibrahi, mai wakiltar mazabar Kwara ta Kudu da ke jihar Kwara, karkashin jam'iyyar PDP. An cafke Sanata Ibrahim, wanda ke neman tazarce, ana gobe zaben shugaban kasa da 'yan majalisun tarayya.

Legit.ng Hausa ta ruwaito cewa cafke Sanata Rafiu ta biyo bayan wani rikici da ya barke a garin Ojuku da ke a mazabar Kwara ta Kudu, wanda har ya sa jam'iyyar APC ta tayar da jijiyoyin wuya tare da bukatar rundunar 'yan sanda ta cafke sanatan a matsayin silar barkewar rikicin.

Akalla mutane biyu ne aka kashe a wajen barkewar rikicin, yayin da mutane da dama suka jikkata, rikicin da jam'iyyar PDP da APC ke caccakar junansu, da kuma zargin juna da zama silar barkewar rikicin.

KARANTA WANNAN: Bauchi 2019: Yadda aka rarraba kayan zabe a kananan hukumomi 20 na jihar Bauchi

Da duminsa: Rundunar 'yan sanda ta cafke Sanata Rafiu Ibrahim ana gobe zabe

Da duminsa: Rundunar 'yan sanda ta cafke Sanata Rafiu Ibrahim ana gobe zabe
Source: Twitter

Da ya ke tsokaci kan cafke sanatan, Muideen Abdulrahma, shugaban kungiyar matasan jam'iyyar PDP na mazabar Kwara ta Kudu, ya ce hakan alama ce ta cewar rundunar 'yan sanda na taka rawar kidan jam'iyyar APC.

Shima da ya ke tofa nashi albarkacin bakin kan cafke sanatan, Mr Olu Onemola, hadimin shugaban majalisar dattijai na kasa, Sanata Bukola Saraki, ya yi Allah-wadai da wannan mataki da rundunar 'yan sandan ta dauka.

Mr Onemola ya ce cafke sanatan alama ce karara da ke bayyana cewa gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari ba ta dauki demokaradiyyar kasar a bakin komai ba, kuma tana amfani da rundunar 'yan sanda domin cimma muradin jam'iyyar APC na siyasa.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel