Jihar Buhari, Katsina ta tserewa dukkan sauran jihohi 35 wajen yawan karban katin zabe

Jihar Buhari, Katsina ta tserewa dukkan sauran jihohi 35 wajen yawan karban katin zabe

Jihar Katsina ta zarcewa dukkan jihohin Najeriya 35 da Abuja wajen yawan karban katin zabe a zaben da za'a gudanar ranan Asabar, 23 ga watan Febrairu da 9 ga Maris, 2019.

Wannan na kunshe ne cikin lissafin da hukumar gudanar da zabe ta kasa mai zaman kanta wato INEC ta saki ranan Alhamis bayan hira da manema labarai a dakin taron ICC Abuja.

Daya daga cikin manyan yan takaran zabe, shugaba Muhammadu Buhari, haifaffen da jihar Katsina ne kuma a jihar zai kada kuri'arsa ranan Asabar.

Lissafin ya nuna cewa kashi 98.7 cikin 100 da sukayi rijista a jihar Katsina ne suka karbi katunansu; sai kuma jihar Taraba inda kashi 97.3 cikin 100 suka karba.

Babban abokin hamayyar shugaba Buhari a wannan zaben dan jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP), Atiku Abubakar.

Atiku haifaffen da jihar Adamawa ne kuma ana kyautata zaton zasu fatata a jihar saboda kwamitin kamfen shugaba Buhari sun bayyana cewa Buhari zai tabuka wani abu a jihar.

KU KARANTA: Zaben 2019: Za'a kulle dukkan iyakokin Najeriya ranar Juma'a

Sauran jihohin da akalla kashi 90 na mutane sun karbi katunan zabensu sune Adamawa (90.7 %), Akwa Ibom (91.2 %), Bauchi (94.8 %), Benue (90.5 %), Cross River (90.8 %), Enugu (92 %), Gombe (96 %), Kaduna (93 %), Kebbi (95.1 %), Niger (91 %), Sokoto (91 %), Yobe (92.4 %), and Zamfara (94.7%).

Jihohin da suke baya-baya a karban katuna sune Ogun (71.3%), Ekiti (73.2%), Imo (74.9%), Oyo (74.1%) and Osun (75.3%).

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel