Ba bu ruwan ku da ra'ayin siyasa - Shugaban hafsin sojin sama ya gargadi Dakaru

Ba bu ruwan ku da ra'ayin siyasa - Shugaban hafsin sojin sama ya gargadi Dakaru

- Shugaban hafsin sojin sama na Najeriya ya jaddada cewa hukumar sa ba ta wani ra'ayi ko kuma rinjaye na akidar siyasa yayin da babban zaben kasa ya gabato

- Air Marshal Sadique ya gana da manyan dakarun sojin sama domin shimfida tsare-tsare na sauke nauyin da rataya a wuyan su cikin lokutan zabe

- Sadique ya kirayi dakarun sojin sama da su hada gwiwa da sauran hukumomin tsaro wajen tabbatar da babban zabe ya gudana cikin tsari da lumana ta kwanciyar hankali.

A yayin babban zaben kasa ke daf da gudana, hukumar dakarun sojin sama ta Najeriya ta daura damara gami da zage dantse wajen tabbatar da ingancin aiki yayin sauke nauyin da rataya a wuyan ta a lokutan zabe cikin kasar nan.

Air Marshal Sadique Abubakar
Air Marshal Sadique Abubakar
Source: Depositphotos

A jiya Alhamis, 21 ga watan Fabrairun 2019, hukumar dakarun sojin sama ta Najeriya ta gudanar da wani muhimmin taro na manyan jami'an ta bisa jagorancin na shugaban ta, Air Marshal Sadique Abubakar, domin shimfida tsare-tsare na tunkarar babban zaben kasa.

Jaridar Legit.ng ta ruwaito cewa, ganawar manyan dakarun sojin sama ta gudana da manufa ta fadakarwa da wayar da kan dukkanin jami'anta kan kauracewa ra'ayi da akidu na siyasa yayin sauke nauyin da ya rataya a wuyan su a lokuta na zaben kasa.

KU KARANTA: Gwamnatin Buhari ta gaza - Kungiyar Kiristocin Najeriya reshen Adamawa

Baya ga gargadi na haramcin nuna akidar su ta siyasa, hukumar rundunar sojin ta kuma nemi dakarun ta akan hada gwiwa da sauran hukumomin tsaro domin tabbatar da gudanar babban zaben kasa cikin lumana da kwanciyar hankali.

A gobe Asabar, 23 ga watan Fabrairun 2019, za a gudanar da babban zabe na kujerar shugaban kasa da kuma na 'yan majalisun tarayya bayan da hukumar zaben ta kasa mai zaman kanta ta dage shi a makon da ya gabata.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na zaurukan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit

Online view pixel