Akwai makarkashiya: Cafke sanata Rafiu Ibrahim ana gobe zabe - Hadimin Saraki

Akwai makarkashiya: Cafke sanata Rafiu Ibrahim ana gobe zabe - Hadimin Saraki

- Wani hadimin Sanata Bukola Saraki, ya yi Allah-wadai da matakin da rundunar 'yan sanda ta dauka na cafke sanata Rafiu Ibrahim ana saura kwana daya zaben kasar

- Mr Olu Onenola ya ce hakan alama ce karara da ke nuni da cewar gwamnatin shugaba Buhari ba ta dauki demokaradiyya a bakin komai ba

- Cafke sanata Rafiu ta biyo bayan wani wani rikici da ya barke a garin Ojuku, da ke mazabar Kwara ta Kudu, mazabar da sanatan ke wakilta

Mr Olu Onenola, hadimin shugaban majalisar Dattijai, Sanata Bukola Saraki, ya yi Allah-wadai da matakin da rundunar 'yan sanda ta dauka na cafke sanata Rafiu Ibrahim ana saura kwana daya zaben shugaban kasa da 'yan majalisun tarayya na kasar.

Mr Olu Onenola, wanda ya bayyana rashin jin dadinsa kan cafke sanata Rafiu a shafinsa na Twitter, ya ce hakan alama ce karara da ke nuni da cewar gwamnati mai ci a yanzu karkashin shugaban kasa Muhammadu Buhari ba ta dauki demokaradiyya a bakin komai ba.

Hadimin shugaban majalisar dattijan, ya zargi gwamnatin Buhari da cusawa hukumomin tsaro a jihohi ra'ayin juam'iyyar, da kuma gudanar da ayyuka a madadinta, domin taimakawa jam'iyyar wajen cimma muradunta na kashin kanta.

KARANTA WANNAN: Bauchi 2019: Yadda aka rarraba kayan zabe a kananan hukumomi 20 na jihar Bauchi

Akwai makarkashiya: Cafke sanata Rafiu Ibrahim ana gobe zabe - Hadimin Saraki
Akwai makarkashiya: Cafke sanata Rafiu Ibrahim ana gobe zabe - Hadimin Saraki
Source: Twitter

Rahotannin da Legit.ng Hausa ta tattara, sun bayyana cewa rundunar 'yan sanda ta cafke Sanata Rafiu Ibrahim, wahda ke neman tazarce a karkashin inuwar jam'iyyar PDP, domin ci gaba da wakiltar mazabar Kwara ta Kudu a majalisar dattijai ta kasa.

Cafke sanatan ta biyo bayan wani umurni da jam'iyyar APC ta baiwa rundunar 'yan sanda a kwanaki biyu da suka gabata na damke Mr Rafiu biyo bayan wani rikici da ya barke a garin Ojuku, da ke mazabar Kwara ta Kudu.

Akalla mutane biyu ne aka kashe yayin da jama'a da dama suka jikkata a yayin da rikicin ya barke, wanda jam'iyyar APC da PDP ke alakanta junansu da alhakin haddasa rikicin.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Online view pixel