Dan majalisar APC a Benue ya sauya sheka zuwa PDP, ya bayar da hujja

Dan majalisar APC a Benue ya sauya sheka zuwa PDP, ya bayar da hujja

- Dan majalisa a jihar Benue, Joseph Bako, mai wakiltan Kwande ta yamma a jihar, ya sauya sheka daga jam’iyyar APC zuwa PDP

- Bako ya sha alwashin aiki don ganin nasarar sabuwar jam'iyyarsa a zabe mai zuwa

- Dan majalisar ya sanar da barinsa APC bayan an rantsar da shi a matsayin dan majalisa

Wani dan majalisa a jihar Benue, Joseph Bako, mai wakiltan Kwande ta yamma a jihar, ya sauya sheka daga jam’iyyar All Progressives Congress (APC) zuwa Peoples Democratic Party (PDP) a wani gangami da aka yi a Adikpo, a ranar Alhamis, 21 ga watan Fabrairu.

Ya bayyana cewa zai yi aiki domin ganin nasarar jam’iyyar a zabuka masu zuwa.

Dan majalisar APC a Benue ya sauya sheka zuwa PDP, ya bayar da hujja

Dan majalisar APC a Benue ya sauya sheka zuwa PDP, ya bayar da hujja
Source: UGC

An rantsar da Boko a matsayin mamba na majalisar dokokin jihar Benue a ranar 12 ga watan Fabrairu, bayan wani dogon shari’a da aka yi a kotu.

Dan majalisar ya sanar da barinsa APC bayan an rantsar da shi a matsayin dan majalisa.

Jam’iyyar ta nuna masa wariya sannan ya kwashe tsawon shekaru uku da rabi yana neman a bi masa hakkinsa a kotu.

KU KARANTA KUMA: Ku fita ku yi zabe – Buhari ga yan Najeriya

A wajen gangamin a ranar Alhamis, 21 ga watan Fabrairu, Boko yace ya bar APC ne saboda yadda aka yi dashi da kuma yaudarar shugabanninta.

Ya yaba ma gwamna Samuel Ortom kan goyon bayan da ya bashi wajen ganin an dawo masa da kujerarsa da aka sace a majalisar dokokin jihar, sannan ya sha alwashin aiki don nasarar jam’iyyar a zabe mai zuwa.

Shafin NAIJ.com Hausa ne ya koma LEGIT.ng Hausa

Latsa kuga sabuwar manhajar Legit.ng Hausa a wayarku ta salula: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafukanmu na dandalin sada zumunta sune:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel