Kungiyoyin direbobi sun rage farashi don mataiya su samu su kai gida don zabe

Kungiyoyin direbobi sun rage farashi don mataiya su samu su kai gida don zabe

- Kungiyar matafiya yankin jihar Oyo tayi kira ga 'ya'yanta da su kasance masu biyyaya bisa hukuncin data zartar

- Kungiyar ta nemi ayiwa duk wani matafiyi ragin 50% na abinda zai biya matukar akwai katin zabe tare dashi

- Kungiyar ta gana da direbobin ta a ranar Alhamis inda ta nemi hadin kansu a bisa hakan

Kungiyoyin direbobi sun rage farashi don mataiya su samu su kai gida don zabe

Kungiyoyin direbobi sun rage farashi don mataiya su samu su kai gida don zabe
Source: Facebook

Kungiyar direbobin motoci (NURTW) yankin jihar Oyo tayi kira ga 'ya'yan ta da suyi biyayya bisa dokar data zartar na ragin 50% ga duk wani matafiyi.

Alhaji Rasheed Oladele mataimakin ciyaman na NURTW ya bayyanawa manema labarai cewa duk wani wanda zaiyi tafiya a Ibadan ya nuna katin zaben sa to rabin kudin kawai zai biya.

Yace kungiyar ta samu ganawa da direbobin ta a ranar Alhamis inda ta nemi goyan bayan su akan wannan kudiri.

GA WANNAN: An bindige har lahira, wani masoyin Buhari a Birnin Nsukka

Mr Matthew Ogundiran ya bayyana cewa shi matafiyi ne daya ce tashar mota da katin zaben sa a lokacin da yaji ragin da aka samu.

Ogundiran yace a maimakon ya biya N1000 zuwa jihar Legas ya biya N500.

Wata fasinja mai suna Mrs Simiat Abiodun ta bayyana cewa kasancewar bata da katin zabe ta biya N1000 a kudin motar tafiya zuwa Legas.

Shafin NAIJ.com Hausa ne ya koma LEGIT.ng Hausa

Latsa kuga sabuwar manhajar Legit.ng Hausa a wayarku ta salula: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafukanmu na dandalin sada zumunta sune:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel