An dawo da 'yan Najeriya 166 daga Libya, an kamo masu kai su su bautar su biyu

An dawo da 'yan Najeriya 166 daga Libya, an kamo masu kai su su bautar su biyu

- An kama mutane biyu da ake zargin su da sana'ar safarar mutane

- Tuni aka mika su ga NAPTIP don cigaba da bincike akan su

- An shawarci wadanda aka dawo dasu gida da su maida hankalin su wajen inganta rayuwar su

An dawo da 'yan Najeriya 166 daga Libya, an kamo masu kai su su bautar su biyu

An dawo da 'yan Najeriya 166 daga Libya, an kamo masu kai su su bautar su biyu
Source: Depositphotos

An kama mutane biyu da ake zargin su da safarar yan Najeriya zuwa Libya da alkawarin zasu kaisu Turai a ranar juma'a.

Wadanda ake zargin da aka boye sunayen su, an kama su ne bayan da wadanda suka yaudaran aka dawo dasu gida kuma ake karbar bayanan su.

Mr Ibrahim Farinloye, mai magana da yawun cibiyar taimakon gaggawa ta NEMA, ofishin yankin kudu maso yamma, ya tabbatar da cigaban ga abinda manema labarai a Legas.

Farinloye yace wadanda ake zargin da safarar mutanen an mika su ga jami'an NAPTIP don cigaba da bincike.

Kamar yanda ya fada, mutane biyu daga cikin jerin wadanda suka dawo a karon farko sun dawo ne of ta filin saukar jirgi na Murtala Muhammed dake Legas.

Yace an dawo da yan Najeriya ne da taimakon IOM da EU tare da hadin guiwar Voluntary Returnees Programme wacce zata kammala aiyukan ta a watan Afirilu na 2020.

Farinloye yace: "Bayan kammala daukar bayanan wadanda aka dawo dasu din, mata 71 sai yara mata 17 da jarirai mata 6. Akwai manyan maza 55 , yara maza 13 da jarirai maza 2. A cikin su akwai uku da suka dawo da matsalar lafiya da kuma mace mai ciki dake nakuda daga dawowar ta Najeriya."

Ya shawarci wadanda suka dawo din dasu maida hankali wajen fara rayuwa mai kyau gani da cewa akwai isassun abubuwan inganta rayuwa a kasar nan a maimakon hangen arzikin dake kasashen ketare.

GA WANNAN: Naira zata ruguzo har N415 ga dala $1 muddin aka kara kudiin mai a bana

Yace duk da hakkin su ne neman abin sawa baki a kasashen waje, amma dole ne su bi hanyar da ta dace da bazata lalata rayuwar su.

Farinloye yace: "Mutum ba zai godewa Ubangiji akan abubuwan dake Najeriya ba har sai ya fita ya bar kasar. Dukkanin ku kunje kuma kun dawo kuma ku yakamata ku bawa wadanda ke hangen can sun labari,"

"Mun gano cewa an yaudari da yawan ku akan damammaki dake kasashen waje kuma yan uwanku na kusa ne. Kuna bukatar tallafi daga gwamnati don shawo kan matsalar safarar mutane daga tushen ta. Ku dinga samar da labarai na masu safarar ga gwamnati.

Masu safarar ba fatalwa bane, kun san su kuma akwai bukatar ku taimakawa matasa dake fadawa cikin irin halin da kuka shiga."

Shafin NAIJ.com Hausa ne ya koma LEGIT.ng Hausa

Latsa kuga sabuwar manhajar Legit.ng Hausa a wayarku ta salula: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafukanmu na dandalin sada zumunta sune:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng News

Mailfire view pixel