A lokacin da ake dab da shiga zabuka, wata kwamishiniya ta tsallake rijiya da baya

A lokacin da ake dab da shiga zabuka, wata kwamishiniya ta tsallake rijiya da baya

- Wata tsohuwar kwamishina ta tsallake rijiya da baya a lokacin da akakai mata hari domin kashe ta

- Maharan sun yankewa mijinta yatsun hannun sa guda Biyar

- Maharan sun samu nasarar shiga gidan ta ne bayan sun kashe wutar lantarki ta hanyar kashe janaretan dake aiki a lokacin

A lokacin da ake dab da shiga zabuka, wata kwamishiniya ta tsallake rijiya da baya

A lokacin da ake dab da shiga zabuka, wata kwamishiniya ta tsallake rijiya da baya
Source: UGC

Wata tsohuwar kwamishina a jihar Ekiti Mrs Funke Owoseeni ta tsallake rijiya da baya bisa wani hari da aka kai mata a muhallinta dake Ijesa Isu dake karamar hukumar Ikole dake jihar a ranar Alhamis.

Maharan wadanda suka kaiwa tsohuwar kwamishinar samame dauke da munanen makamai sun illata mijinta Mr Paul Owoseeni a lokacin da basu sameta ba.

Sun rufarwa Mr Owoseeni da adda da sauran munanan makamai har saida suka cire masa yatsun hannun sa guda Biyar.

Mrs Owoseeni wadda ta rike mukamin caretaker chairman a Ikole sannan kuma ta rike mukamin woman leader a jam'iyar APC a jihar ta bayyana wa manema labarai yanda abin ya afku ta wayar tafi da gidanka inda tace

"Makisan sun isa gidanta ne da misalin 8:30pm kuma suka datse wutar lantarkin gidan ta hanyar dakatar da injin janaretan dake aiki a lokacin sannan suka shiga gidan".

"A lokacin da wasu dalibai da suke zaune waje daya dasu suke kokarin gyara wutar ne makisan suka ritsasu suna tambayar su ina Mrs Owoseeni take a lokacin".

GA WANNA: Bayan Ghana, Italiya ma ta fara koro 'yan Najeriya saboda kananan laifuka daga zuwansu

"Bayan shudewar wasu mintuna sai muka fara jiyo muryoyin su suna cewa ' Ku taimaka mana' sai mijina ya fita dan ganin abinda ke faruwa ni kuma nayi kokarin daukar torchlight saboda naga abinda yake gudana sosai.

"A wannan lokaci ne naji abinda yake gudana sai na gudu naje na buya su kuma suka taso mijina a gaba suna tambayar sa inda nake a yayin da yaki fada musu shine suka rufar masa har suka cire masa yatsun hannun sa."

Mrs Owoseeni ta bayyana cewa sunyi gaggawar mika mijin nata zuwa babban asibitin jihar kafin daga bisani a maidoshi Ekiti state university teaching hospital dan samun kyakkyawar kulawa.

Hukumar yan sandan jihar sun bayyana cewa ba'a kai musu rahoton faruwar wannan abu ba.

Shafin NAIJ.com Hausa ne ya koma LEGIT.ng Hausa

Latsa kuga sabuwar manhajar Legit.ng Hausa a wayarku ta salula: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafukanmu na dandalin sada zumunta sune:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel