Zabe: Bai kamata ku bari APC ta razana ku da bindiga ba, ku fito kuyi zabe

Zabe: Bai kamata ku bari APC ta razana ku da bindiga ba, ku fito kuyi zabe

- Jam'iyyar PDP ta hori yan Najeriya masu kada kuri'a da kada su tsorata da umarnin shugaban kasa

- Shugaban PDP na kasa yace yan Najeriya su maida hankali kuma tare da nuna rashin damuwa yayin da suka fita kada kuri'a

- An hori yan Najeriya da su gwadawa Afirka da duniya baki daya cewa burin mu farfado da damokaradiyyar mu

Zabe: Bai kamata ku bari APC ta razana ku da bindiga ba, ku fito kuyi zabe

Zabe: Bai kamata ku bari APC ta razana ku da bindiga ba, ku fito kuyi zabe
Source: Facebook

Jam'iyyar PDP ta hori masu kada kuri'a da kada su tsorata da umaranin da shugaba Buhari ya bawa sojoji na harbe barayin zabe.

A ranar litinin ne shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bawa sojin Najeriya da sauran jami'an tsaro umarnin sabawa barayin akwatin zabe yayin zaben shugaban kasa da na majalisar dattawa.

Shugaban PDP, Prince Uche Secondus yayin bayani ga kafafen yada labarai a Abuja a jiya, ya hori yan Najeriya da su maida hankalo tare da nuna halin rashin damuwa yayin da suka suka fita kada kuri'un su.

Shugaban jam'iyyar ya kwatanta umarnin shugaban kasar a matsayin shirin magudi a sakamakon zabe.

Secondus yace: "Lokacin da shugaban kasa yayi wa hukumar zabe mai zaman kanta barazana bayan an dage zaben, niyyar shi itace tsoratar dasu don suyi biyayya ga abinda APC ke so.

"Lokacin da suke hantara, kamawa da rufe asusun bankunan masu ruwa da tsaki yan adawa, suna so suyi nasara ne kota halin yaya. Lokacin da suka soji a harkar siyasa, burin su kiri kiri shine su lalata hukumar sojin yanda suka fita yiwa mahukunta da masu shari'a a kasar nan,"

GA WANNAN: Bayan an nemi N10,000,000 an rasa a karkashin kulawarsa, EFCC ta cafko shi yayi bayani

"Amma ina horar yan Najeriya da kada su tsorata ko suji haushi, su kawai maida hankali akan nasarar dake tunkaro mu a ranar asabar."

Shugaban ya roki masu ruwa da tsaki a zaben nan, ballantana INEC, jami'an tsaro da wakilan jam'iyyun siyasa da su tuna Najeriya farko kafin komai.

"Zaben za'ayi ne don ceto kasar nan da kuma Raya raya damokaradiyyar mu."

Shugaban kwamitin tsare tsare na kungiyar kamfen din shugaban kasa karkashin jam'iyyar PDP, Osita Chidoka, yace duniya idon ta na kan Najeriya kuma ya hori masu zabe da su zama masu hakuri, zaman lafiya da juriya.

Ya roki yan Najeriya dasu gwadawa Afirka da duniya baki daya cewa kasar mu na shirye don habaka damokaradiyyar mu da mulki karkashin doka.

Chidoka yace PDP ta koyi darasi a zaben da ya gabata kuma a shirye take don bawa yan Najeriya karfin guiwa cewa kuri'un su zasu yi amfani.

Kamar yanda ya fada, PDP shirye take tsaf don jajircewa duk wata tsoratarwa ta bangaren jami'an tsaro.

Shafin NAIJ.com Hausa ne ya koma LEGIT.ng Hausa

Latsa kuga sabuwar manhajar Legit.ng Hausa a wayarku ta salula: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafukanmu na dandalin sada zumunta sune:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel