Anyi kira ga shugaba Buhari da ya janye soji daga gaban akwatunan zabe a gobe

Anyi kira ga shugaba Buhari da ya janye soji daga gaban akwatunan zabe a gobe

- Kada sojoji su shiga harkar zabe sai dai ko jihohi dake fama da hare haren yan ta'adda

- Babu dokar da tace a kashe masu laifi yayin zabe, inji shugabar CDD

- Daga lura da da jawabai da bincike, sun nuna cewa INEC ta shirya tsaf tsaf don zaben ranar asabar

Anyi kira ga shugaba Buhari da ya janye soji daga gaban akwatunan zabe a gobe

Anyi kira ga shugaba Buhari da ya janye soji daga gaban akwatunan zabe a gobe
Source: Twitter

Kada sojoji su shiga harkar zai sai dai a jihohin dake fama da hare haren ta'addanci, inji EAC ta hukumar CDD.

Cibiyar ta sanar da hakan ne a alhamis yayin jawabi ga manema labarai akan shirye shiryen hukumar zabe mai zaman kanta na zaben da aka dage.

Hakan maida martani ne ga maganar shugaba Buhari ta ranar litinin da yace a sabawa barayin akwatin zabe.

Daraktan CDD, Idayat Hassan wacce tayi magana da yawun kungiyar, tace "Babu manyan ladaftarwa game da laifukan zabe."

"Dokokin a bayyane suke, masu laifi yayin zabe zasu zauna gidan kaso ne na shekaru biyu ko su biya tarar Naira 500,000. Babu inda aka ce a kashe su kamar yanda shugaban kasar ya fada," inji ta.

Tace: "Tururuwar fitowa don zabe na raguwa ne tun a shekarar 1999, har ta kai ga idan muka samu kashi 45 a zabukan nan, mun samu cigaba akan abinda aka samu yayin zaben 2015."

An samar da EAC ne a 11 ga watan Fabrairu a matsayin cibiyar kididdiga da kashe labaran kanzon kurege yayin zabe.

Cibiyar ta shawarci yan sanda dasu tsaya da tura jami'an su don gujewa nuna abinda ba shi kenan ba yayin karatowar zaben.

"Duk da abubuwan dake tasowa, duba da mukayi da bayanan Farfesa Yakubu, tare da dubban masu lura, mun gano cewa hukumar zabe ta shirya tsaf don zaben ranar asabar," inji ta.

GA WANNAN: Naira zata ruguzo har N415 ga dala $1 muddin aka kara kudiin mai a bana

"Duk da hakan, akwai aiyuka da yawa da yakamata ayi, wadanda zasu tabbatar da an shawo kan duk wasu matsaloli na raba kayan aiki da jami'ai ga kananan hukumomi sun kammala babu bata lokaci."

Cibiyar ta nuna damuwar ta akan dawo da tare da kai kayayyakin zaben da aka kaisu inda bai dace ba.

Don samun tatattun labarai, CDD da EAC tace ta tura masu lura da kwarraru don maida hankali ga tattaunawar kungiyoyi tare da hira da masu ruwa da tsaki.

Sunce harin Boko Haram a jihar Yobe da Maiduguri da suka samu rahoton su daga masu lura da kwarraru abin tashin hankali ne.

Dubawar cibiyar ta nuna cewa aikin yan ta'adda a Zamfara da rahoton garkuwa da mutane a kananan hukumomin Shiroro da Raffi zasu iya shafar tura jami'an zabe masu lura da zabukan da kuma ma'aikatan INEC yankunan.

Cibiyar tace yakamata hukumomin tsaro su duba cewa yayin tura jami'an tsaro garuruwan dake fama fama da hare hare, kada su tura jami'ai fiye da ka'ida ta yanda zasu tsorata masu zabe.

Shafin NAIJ.com Hausa ne ya koma LEGIT.ng Hausa

Latsa kuga sabuwar manhajar Legit.ng Hausa a wayarku ta salula:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafukanmu na dandalin sada zumunta sune:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel