Ina mazan suke: Yadda wasu Mata suka yi arangama da masu garkuwa da mutane suka samu nasara

Ina mazan suke: Yadda wasu Mata suka yi arangama da masu garkuwa da mutane suka samu nasara

Wasu gungun Mata sun yi namijin kokari wajen tseratar da wata tsohuwa da wasu barayin mutane suka yi kokarin yin garkuwa da ita a garin Jalingo na jahar Taraba, bayan sun yi arangama dasu a tsakiyar titi, kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito da misalin karfe 6:45 na yammacin ranar Alhamis ne wasu gungun barayin mutane su biyar suka kama wata mata mai suna Malama Haruna suka jefata a cikin Keke Napep din da suke ciki, inda suka yi kokarin tserewa da ita.

KU KARANTA: Gwamnatin jahar Kano ta garkame ofishin Sheikh Daurawa na sakatariyar Hisbah

Rahotanni sun bayyana cewa Malama ta fito ne da nufin yin rakiya ga wata mata mai suna Nana Aisha data kai mata ziyara, zuwa bakin titi don ta hau KEKE Napep a lokacin da lamarin ya faru, sai dai Malama ba tayi shiru ba, inda ta shiga kwarmata ihu tana neman agaji.

Nan da nan mata da kananan yara suka taso suka tunkari Keken, inda suka shiga kokawa da barayin suna dukansu duk da cewa Keken bai tsaya ba, har sai da suka samu nasarar kwato Malama, sa’annan suka ladaka ma barayin dan banzan duka.

Rahotanni sun bayyana cewa a yan kwanakin nan barayin mutane sun bude wuta da satar mutane a garin Jalingo na jahar Taraba, inda suka sace Mata da dama, kuma suna yin amfani da Keke Napep ne wajen aikata wannan mummunan aiki.

Sai dai majiyarmu bata samu jin ta bakin kaakakin rundunar Yansandan jahar Taraba, ASP David Misal ba, sakamakon lambar wayarsa bata shiga a lokacin da wakilai suka kirashi domin jin tsokacinsa.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit.ng News

Mailfire view pixel