Gwamnatin jahar Kano ta garkame ofishin Sheikh Daurawa na sakatariyar Hisbah

Gwamnatin jahar Kano ta garkame ofishin Sheikh Daurawa na sakatariyar Hisbah

Wasu bayanai dangane da tsatstsamar dangantakar data kunno kai a tsakanin gwamnan jahar Kano, Abdullahi Umar Ganduje da kuma tsohon gwamna Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, wanda ke nuni da rikicin yayi naso, kuma har ya shafi Sheikh Aminu Daurawa.

Sheikh Daurawa shine dai shugaban hukumar Hisbah, mukamin da yake rikewa tun a zamanin mulkin Gwamna Kwankwaso, inda bayan lashe zabensa, Gwamna Ganduje ma ya barshi akan wannan mukami, amma a yanzu ana kishin kishin zai saukeshi, don kuwa har an garkame ofishinsa dake Hisbah.

KU KARANTA: Da dumi dumi: Mutane da dama sun mutu yayin da aka kai ma Kwankwaso hari a jahar Kano

Sai dai wasu abubuwa sun faru a baya tsakanin Daurawan kansa da Gwamna Ganduje, musamman bayan ballewar rikicin siyasa tsakanin Gandujen da Kwankwaso, inda gwamnan da mukarrabansa ke ganin kamar Daurawa ya fi karkata ga Kwankwaso fiye da Ganduje.

Guda daga cikin irin wannan lamari shine lokacin da wasu fayafayan biyo suka bayyana a shafukan yana gizo dake nuna yadda Gwamna Ganduje ke karbar daloli yana antayawa a cikin aljihu, inda bayan bayyanan bidiyon aka jiyo Malam Daurawa yana sukar irin wannan halayya.

Haka zalika mutumin da ake zargi da fallasa bidiyoyin ya nemi ya gurfana gaban majalisar dokokin jahar Kano domin ya amsa tambayoyi, amma sai ya gindaya sharadin kasancewar Daurawa a majalisar a lokacin da zai gurfana.

Na baya bayannan kuma shine cacar baki da ta kaure tsakanin Sanata Kwankwaso da wasu Malaman Izalan jahar Kano, wannan rikici ya samo asali ne daga kiran da shugaban Izalan Kano, Saleh Pakistan ya yi dake nuna jama’a su zabi Ganduje a matsayin gwamnan jahar Kano.

Sai dai wannan magana bata yi ma Kwankwaso dadi ba, inda shima ya bara, wanda hakan ya nemi ya hargitsa farfajiyar siyasar jahar Kano, ana cikin haka kuma sai Daurawa ya jagoranci tawagar Malamai 100 zuwa gidan Sanatan don yin sasanci, kamar yadda ya bayyana.

Legit.ng ta ruwaito garkame ofishin Malamin baya rasa nasaba da wadannan abubuwa, musamman ma ziyarar gidan Sanatan da Malamin ya kai, inda majiyoyi suka tabbatar da tuni aka sauya ma sakataren Daurawan wajen aiki a cikin hukumar Hisbah.

Sai dai Malamin ya bayyana cewa bashi da wata masaniya game da hakan, sakamakon ya mika makullin ofishinsa ga mataimakinsa kafin ya wuce aikin Umarah a kasar Saudiyya, kuma har yanzu babu wanda ya bashi makamancin wannan labari.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel