PDP ta yi jan kunne ga Buhari da Ganduje idan har wani abu ya samu Kwankwaso

PDP ta yi jan kunne ga Buhari da Ganduje idan har wani abu ya samu Kwankwaso

Shugaban jam’iyyar PDP, Uche Secondus ya bayyana damuwarsa da harin da yace yan barandan jam’iyyar APC dana gwamnan jahar Kano Abdullahi Umar Ganduje suka kai ma Sanata Rabiu Kwankwaso, inda ya ja kunnensu game da sake faruwar wani abu irin haka.

A ranar Alhamis, 21 ga watan Feburairu ne aka yi kare jini biri tsakanin magoya bayan Kwankwasiyya da na Abdulmuminu Jibrin, dan majalisa mai wakiltar Kiru da Bebeji a majalisar tarayya, a garin Kofa, inda aka kashe mutane biyar, aka kona motoci da dama, tare da jikkata wasu da dama.

KU KARANTA: Da dumi dumi: Mutane da dama sun mutu yayin da aka kai ma Kwankwaso hari a jahar Kano

Sai dai Legit.ng ta ruwaito Secondus na cewa manakisa aka shirya tare da wasu yan daba da nufin halaka Kwankwaso, don haka yace akwai bukatar shugaban kasa Muhammadu Buhari da Gwamna Ganduje su yi bayanin shirin da suka yi na halaka Kwankwaso.

Haka zalika Secondus ya nemi a kafa kwamitin bincike na musamman mai zaman kanta domin gano wadanda keda hannu cikin wannan hari da yan APC suka kai ma Kwankwaso, sa’annan yayi kira ga kasashen duniya dasu ankara da hamayyar da APC ke nuna ma Kwankwaso.

“Muna ganin wannan hari baya rasa nasaba da umarnin da shugaban kasa Buhari ya bayar na kashe duk wanda ya saci akwatin zabe, da barazanar da shugaban hafsan sojan kasa ya yin a dabbaka wannan umarni.

“Sun tsara kashe Kwankwaso ne saboda hakan zai iya tayar da hankali a jahar Kano, ta yadda ba za’ayi zaben 2019 a jahar ba, musamman bayan sun lura da jama’an da jam’iyyar PDP ta tara a yayin gangaminta, wanda hakan manuniyace ga nasarar da PDP za ta samu a jahar APC.” Inji shi.

Bugu da kari, shugaban PDP yayi zargin gwamnatin Najeriya na shirin kama jiga jigan yayan jam’iyyar PDP a jihohin Jigawa, Katsina, Kano, Rivers, Kwara, Akwa Ibom, Bauchi da kuma jahar Kogi don su karya lagon jam’iyyar.

Daga karshe yayi kira ga kwamishinan Yansandan jahar Kano, Muhammad Wakili daya tabbata ya kama duk wadanda keda hannu cikin harin da aka kai ma Kwankwaso, tare da gurfanar dasu gaban kuliya manta sabo domin ta hukuntasu.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit.ng

Online view pixel