Gwamnatin Buhari ta gaza - Kungiyar Kiristocin Najeriya reshen Adamawa

Gwamnatin Buhari ta gaza - Kungiyar Kiristocin Najeriya reshen Adamawa

Kafar watsa labara ta Sahara Reporters ta ruwaito cewa, ganawar mataimakin shugaban kasa, tare da kungiyar Kiristocin Najeriya reshen jihar Adamawa ba ta haifar da wani da mai ido ba yayin da ya gaza ba su dalilai na goyon bayan shugaban kasa Buhari.

Mun samu cewa, an tashi baram-baram yayin ganawar mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo da kungiyar Kiristocin Najeriya ta CAN reshen jihar Adamawa, sakamakon gazawar sa ta bayar da dalilai na goyon bayan shugaban shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Gwamnatin Buhari ta gaza - Kungiyar Kiristocin Najeriya reshen Adamawa

Gwamnatin Buhari ta gaza - Kungiyar Kiristocin Najeriya reshen Adamawa
Source: Twitter

Rahotanni sun bayyana cewa, Farfesa Osinbajo ya tattaki zuwa birnin jihar Yola na jihar Adamawa domin neman mabiya addinin sa na Kirista su goyi bayan jam'iyyar APC yayin da babban zaben kasa ke daf da gudana.

Osinbajo ya ziyarci jihar biyo bayan rade-radin dan takarar kujerar shugaban kasa na jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar da ya bayyana cewa, akwai yiwuwar babban zaben kasa na ranar Asabar ba zai gudana ba cikin wasu jihohi uku da suka hadar da Adamawa, Borno da kuma Kaduna.

Majiyar jaridar Legit.ng ta ruwaito cewa, Mataimakin shugaban kasa ya sha kunyar gaske yayin da kungiyar ta nemi masaniya tare da dalilai dangane da yadda gwamnatin shugaban kasa Buhari ta gaza yaye matsalolin mabiya addinin Kirista da ke fadin kasar nan.

KU KARANTA: Zaben 2019: INEC na fuskantar karancin ma'aikata cikin jihohi 13 na Najeriya

Binciken manema labarai ya tabbatar da cewa, Mataimakin shugaban kasa ya mika kokon barar sa ga kungiyar CAN reshen jihar Adamawa domin neman amincewar ta kan kudirin tazarce na shugaban kasa Buhari, inda ta yi mursisi da cewar ba bu wata moriya da ta ci a gwamnatin sa.

Cikin wani rahoton mai nasaba da wannan, kwanaki uku da suka gabata shugaban kasa Buhari ya kirayi taron gaggawa tare da gwamnonin jihohin Kaduna, Borno, Kaduna da kuma shugabannin tsaro biyo bayan rade-radin babban abokin sa na adawa.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na zaurukan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit

Online view pixel