Gwamnatin Najeriya ta yi wa jakadan kasar Saudiyya kiranye

Gwamnatin Najeriya ta yi wa jakadan kasar Saudiyya kiranye

Ma’aikatar harkokin waje ta yi wa jakadan Najeriya a kasar Saudiyya, Ambasada Muhammad Yunusa, kiranye domin ya dawo hedikwatar ta da ke Abuja domin wasu korafe-korafe da gwamnatin kasar Saudi ta yi a kan sa.

An bukaci Ambasada Yunusa ya dawo gida Najeriya domin ya amsa zargin rashin bawa hukumomin kasar Saudiyya hadin kai, kamar yadda mmajiyar da ta wasikar da aka aike ma sa ta shaida ma na.

Wasikar ta ce rashin bawa hukumomin kasar Saudiyya hadin kai da jakadan na Najeriya ya yi kan iya haifar da rauni ga kyakyawar dangantakar da ke tsakanin kasashen biyu.

A bisa dogaro da ikon da na ke da shi a matsayina na minister, alhakina ne na yi ma ka kiranye ka dawo hedikwatar domin amsa muhimman tuhume-tuhume cikin gaggawa.

Gwamnatin Najeriya ta yi wa jakadan kasar Saudiyya kiranye

Ministan harkokin kasashen waje ; Geoffrey Onyeama
Source: Facebook

“Yin hakan ya zama wajibi ne domin akwai bukatar ka dawo hedikwata domin bayar da amsoshi ga wasu korafe-korafe da gwamnatin kasar Saudiyya ta yi a kan ka na rashin bas u hadin kai, lamarin da kan iya haifar da rashin jituwa tsakanin kasashen biyu da ke da kyakyawar dangantaka.

DUBA WANNAN: Dalla-dalla: INEC ta yi bayanin yadda za ta biya ma’aikatan wucin gadi

“Ka mika ragamar al’amuran jakadanci ga ma’aikaci ma fi girman mukami a ofishin jakadancin Najeriya a kasar Saudiyya ka dawo gida domin amsa tuhumar da ake yi ma ka,” kamar yadda ya ke a cikin wasikar.

DUBA WANNAN: Dalla-dalla: INEC ta yi bayanin yadda za ta biya ma’aikatan wucin gadi

Saidai wasikar ba ta yi karin bayani a kan irin hadin kan da Ambasada Yunusa ya ki bawa hukumomin kasar Saudiyya ba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Nigeria

Online view pixel