Ni dan jam'iyyar APC ne duk da kasancewa ta kakakin Atiku - Buba Galadima

Ni dan jam'iyyar APC ne duk da kasancewa ta kakakin Atiku - Buba Galadima

Mai magana da yawun kungiyar yakin neman zaben Atiku Abubakar, Injiniya Buba Galadima ya ce har yanzu shi dan jam'iyyar All Progressives Congress (APC) ne.

A hirar da akayi da Galadima a wani shirin Channels TV mai suna 'The Verdict' ya ce har yanzu shi mamba ne na jam'iyyar APC ne kuma shine jagorar 'yan aware na jam'iyyar da akafi sani da Reformed APC.

Buba ya yi wannan fashin bakin ne yayin da mai gabatar da shirin Seun Okinbaloye ya gabatar da shi a matsayin dan jam'iyyar Peoples Democratic Party.

Ni dan jam'iyyar APC ne duk da kasancewa ta kakakin Atiku - Buba Galadima

Ni dan jam'iyyar APC ne duk da kasancewa ta kakakin Atiku - Buba Galadima
Source: Facebook

DUBA WANNAN: Jajiberin zabe: Wani shiri da Atiku ya kulla da jam'iyyu 5 ya samu matsala

"Har yanzu ni dan jam'iyyar APC ne," ya yiwa mai gabatar da shirin gyara.

Tsohon sakataren rusheshiyar jam'iyyar Congress for Progressive Change, ya kara da cewa, "Ni mai magana da yawun dan takarar shugabancin kasa na PDP ne kuma."

Galadima wanda tsohon na hannun daman Buhari ne ya kara da cewa ya yi imanin Atiku zai kayar da Shugaba Muhammadu Buhari a zaben da za a gudanar a ranar Asabar.

Ya ce jam'iyyar PDP ta mulka kusan dukan jihohin arewa saboda haka ba abin mamaki bane ayi tsamanin ba za su lashe zabukkan ba.

Galadima ya ce adadin magoya bayan da suka fito suka nuna wa Atiku goyon baya a Kano da sauran jihohin arewa alama ce da ke nuna cewa mutane na kaunarsa.

Ya yi ikirarin cewa jam'iyyar APC ta dako hayar mutane daga Jamhuriyar Nijar domin ta kara adadin magoya bayan ta a wurin yakin neman zabe a Kano.

"Atiku Abubakar neshugaban kasar Najeriya mai jiran gado da izinin Allah.

"Yan Najeriya dukkansu namu ne babu banbancin addini ko kabilanci.

"Idan anyi adalci a zabe, Atiku ne zai lashe zaben shugabancin kasa da za ayi ranar 23 ga watan Fabrairu," inji shi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel