Jajiberin zabe: Buhari zai gabatar da jawabi ga ‘yan Najeriya da karfe 7:00 na safe

Jajiberin zabe: Buhari zai gabatar da jawabi ga ‘yan Najeriya da karfe 7:00 na safe

Mai taimakawa shugaban kasa Muhammadu Buhari a bangaren yada labarai a kafafen sadarwar zamani, Bashir Ahmad, ya fitar da sanarwar cewar shugaba Buhari zai gabatar da jawabi ga ‘yan Najeriya da safiyar ranar juma’a wanda za a nuna kai tsaye a gidan Talabijin na kasa (NTA) da kuma gidajen Radiyo na kasa da sauran kafafen watsa labarai.

Za a watsa jawabin kai tsaye a gidajen Talabijin da Radiyo da misalin karfe 7:00 na safe sannan a kara maimaita wa da misalin karfe 9:00 na safe.

Wannan shine karo na uku a cikin kasa da kwanaki 10 da shugaba Buhari ya gabatar da jawabi ga ‘yan Najeriya.

Duk da ba a bayyana a kan batun da shugaban kasar zai gabatar da jawabin, ana ganin ba zai rasa nasaba da batun zaben shugaban kasa da na ‘yan majalisar tarayya da za gudanar ranar Asabar, 23 ga watan Fabrairu ba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel