Zaben 2019: INEC na fuskantar karancin ma'aikata cikin jihohi 13 na Najeriya

Zaben 2019: INEC na fuskantar karancin ma'aikata cikin jihohi 13 na Najeriya

Wani bincike da manema labarai na jaridar Sahara Reporters suka gudanar ya bayyana cewa, akwai yiwuwar babban zaben kasa na ranar Asabar zai yi gamo da wani sabon cikas cikin wasu jihohi 13 na Najeriya a sakamakon karancin ma'aikata.

Binciken jaridar Sahara Reporters ya tabbatar da cewa, hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta wato INEC ta yi gamo da karancin ma'aikata sakamakon yadda ta dakatar da wasu manyan ma'ikatan ta kimanin 205 tsawon watanni 22 da suka gabata a cikin wasu jihohin kasar nan.

Wata majiyar rahoton mai sahihancin gaske ta tabbatar da cewa, akwai manyan ma'aikatan hukumar INEC kimanin 205 masu nauyin gudanar da muhimman ayyuka da a halin yanzu su ke ci gaba da fuskantar hukuncin dakatar wa na hukumar tsawon watanni 22 da suka shude.

Shugaban hukumar INEC; Farfesa Mahmood Yakubu

Shugaban hukumar INEC; Farfesa Mahmood Yakubu
Source: Twitter

Rahotanni kamar yadda majiyar jaridar Legit.ng ta ruwaito sun bayyana cewa, akwai yiwuwar zaben kasa na ranar Asabar zai yi gamo da cikas a sanadiyar rashin wannan manyan ma'aikata da kawowa yanzu hukumar INEC ba ta maye guraben su ba.

Daya daga cikin kwamishinonin hukumar INEC na reshen jihar Adamawa, Kashim Gaidam, ya yi korafi tare da koken karancin manyan ma'aikata inda a halin yanzu ake ribatar kananan ma'aikata masu karancin kwarewar wajen gudanar da aikin kwararru.

KARANTA KUMA: Nau'ikan shiga 10 da shugaba Buhari ya yi a tsakanin yakin zaben 2015 da 2019

Kafar watsa labarai ta Sahara Reporters ta bayyana cewa, hukumar INEC na ribatar kananan ma'aikata da suka hadar da masu aikin gadi da goge wajen gudanar da manyan aikace-aikace da suka rataya a wuyan kwararru.

Cikin jerin jihohin da ka iya fuskantar koma baya sakamakon karancin manyan kwararrun ma'aikata sun hadar da; Adamawa, Anambra, Cross River, Delta, Enugu, Gombe, Jigawa, Kano, Legas, Neja, Ogun, Osun da kuma jihar Taraba.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na zaurukan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel