Wata-sabuwa: ‘Yan sanda sun kama mota dankare da kayan zabe a jihar Zamfara

Wata-sabuwa: ‘Yan sanda sun kama mota dankare da kayan zabe a jihar Zamfara

Kwamishinan ‘yan sandan jihar Zamfara Mista Celestine Okoye ya sanar wa da manema labarai a ofishin hukumar zabe dake garin Gusau cewa rundunar ‘yan sandan jihar ta samu nasarar kama wata mota dankare da kayan zabe za a kaisu Sokoto daga Abuja.

Okoye ya ce bincike ya nuna cewa wasu ne da basu da izinin daukan kayan zabe suka loda wannan mota da kayan domin kai su jihar Sokoto. Okoye yace rundunar ta kama motar da direban sannan ta na gudanar da bincike a kai.

Wata-sabuwa: ‘Yan sanda sun kama mota dankare da kayan zabe a jihar Zamfara

Wata-sabuwa: ‘Yan sanda sun kama mota dankare da kayan zabe a jihar Zamfara
Source: Depositphotos

KU KARANTA: An ka wasu 'yan sanda da sojoji suna yiwa Buhari kamfen

Legit.ng Hausa haka zalika ta samu cewa Mista Okoye ya kuma kara tabbatar wa mutane cewa jami’an tsaro ba za su yi kasa kasa ba wajen ganin sun kama duk wadanda bai kamata ya mallaki wani abu na zabe ba.

Ya kara da cewa sun dauki matakan da zai taimaka wajen ganin sun kare duk kayan zaben da za a yi amfani da su a lokacin zabe.

A karshe ita ma jami’ar hukumar zabe na jihar Asma’u Sani Maikudi ta tabbatar da haka.

A cikin makon nan ne hukumar zabe mai zaman kanta na kasa (INEC) ta bayyana cewa ta dawo da kayan zaben da ta fara kaiwa wasu jihohi a kasar nan.

Hukumar ta yi haka ne domin tabbatar da inganci da sahihancin zaben shugaban kasa da na majalisar dattawa, wanda za a gudanar ranar Asabar mai zuwa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma legit.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://web.facebook.com/legitnghausa?_rdc=1&_rdr

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Source: Legit.ng

Tags:
Online view pixel