Da dumin sa: Masu garkuwa sun sace dan wani limamin coci a jihar Filato

Da dumin sa: Masu garkuwa sun sace dan wani limamin coci a jihar Filato

Wasu 'yan bindigar da ba'a tantance ko suwaye ba mun samu labarin cewa sun dira a karamar hukumar Barkin Ladi a jihar Filato dake a shiyyar Arewa ta tsakiya inda suka kuma yi nasarar sace dan wani limamin cocin dake kwalejin kimiya dake karamar hukumar.

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar ta Filato din ne dai, Mista Tyopev Terna ya bayyana hakan a yayain da yake tattaunawa da manema labarai a ofishin sa.

Da dumin sa: Masu garkuwa sun sace dan wani limamin coci a jihar Filato

Da dumin sa: Masu garkuwa sun sace dan wani limamin coci a jihar Filato
Source: Facebook

KU KARANTA: Sakataren gudanarwar PDP ya yi murabus

A cewar Mista Terna, limamin cocin kuma mahaifin yaron Andrew Dido ne ya kawo karar sace dan nasa a hedikwatar ofishin su ranar Alhamis.

”Andrew ya ce masu garkuwan sun far wa gidansa da karfe tara na daren Laraba sannan suka tafi da dansa mai suna Kim Dido mai shekaru 12. Sun kwace wayar dake hannun sa sannan suka bar lambar wayar da za a iya kiransu da shi kamar haka 0803644144.” In ji shi.

Terna ya ce bayan sun samu wannan rahoto sai suka tura jami’an su domin bin dazukan dake kewaye da su domin kamo masu garkuwan a inda suka boye yaron sannan a ceto sa.

Ya kuma ce sun saka jami’an tsaro a wannan makaranta domin samar da tsaro sannan sun yi kira ga mutane da su gaggauta tuntubar jami’an tsaro idan a ka samu bayanan da zai iya taimakawa wajen ceto wannan yaron.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma legit.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://web.facebook.com/legitnghausa?_rdc=1&_rdr

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel