Rikicin jihar Kano: A gaban Kwankwaso yaransa suke kaiwa yan APC hari suna addu'a - Ganduje

Rikicin jihar Kano: A gaban Kwankwaso yaransa suke kaiwa yan APC hari suna addu'a - Ganduje

Gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje, ya yi Allah wadai da harin da yan Kwankwasiyyan jam'iyyar PDP suka kaiwa kaiwa mambobin jamiyyar All Progressive Congress, APC, yayin yakin neman zabe a karamar hukumar Kiru/Bebeji.

Legit Hausa ta kawo muku rahoton cewa akalla matasa biyar sun rasa rayukansu kuma dama sun jikkata a rikici da ta barke tsakanin mambobin jam'iyyar PDP da APC

Akalla motoci 10 aka lalata a rikicin.

Amma gwamnan jihar Kano ta bakin kwamishanan labarai, Muhammad Garba, ya tuhumci yan Kwankwasiyya da tayar da rikicin.

Yace: "Yan Kwankwasiyya sun cigaba da kai hare-hare kan mambobin jam'iyyar All Progressive Congress (APC). Wani ya faru a ranan Alhamis inda mambobinmu ke gudanar da addu'a a karamar hukumar Bebeji kan zabe."

"Kawai sai suka afkawa magoya bayanmu a gaban shugabansu, Rabi'u Kwankwasi, wanda yaje yakin neman zabe yankin."

A karshe yayi addu'a ga wadanda suka rasa rayukansu kuma yana mai jajintawa iyalansu. Kana yana addu'a ga wadanda suka jikkata Allah ya basu lafiya.

Gwamna Ganduje ya umurci jami'an tsari sun binciko wadanda suka aikata wannan aika-aika domin hukunta su.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel