Zaben Asabar mai zuwa: Babu madadin shugaba Buhari - Akpabio

Zaben Asabar mai zuwa: Babu madadin shugaba Buhari - Akpabio

- Sanata Godswill Akpabio ya bayyana cewa idan aka yi la’akari da nasarori da gwamnatin Buhari ta samu, Najeriya za ta ga cewan bata da wani da zai iya maye gurbinsa

- Akpabio yace babu madadin shugaban kasar a zaben da za a gudanar a ranar Asabar mai zuwa

- Jigon na APC ya shawarci yan Kudu da kada su yi kuskuren zabar wanda zai siyar da NNPC

Jagoran kwamitin magoya bayan kudirin shugaban kasa Muhammadu Buhari, sanata Godswill Akpabio ya bayyana cewa idan aka yi la’akari da nasarori da gwamnatin Shugaban kasar ta samu, Najeriya za ta ga cewan bata da wani da zai iya maye gurbinsa illa ma ta sake bashi damar da zai kuma shugabantarta a takara karo na biyu.

Akpabio, wanda yayi magana ga manema labarai a Abuja, ya bukaci mutanen kudancin kasar da su sake tunani akan matsayinsu na shirin zabar jam’iyyar dake son siyar da kamfanin mai na Najeriya (NNPC) da sauran kaddarorin kasar.

Zaben Asabar mai zuwa: Babu madadin shugaba Buhari - Akpabio

Zaben Asabar mai zuwa: Babu madadin shugaba Buhari - Akpabio
Source: UGC

Atiku Abubakar, dan takaran kujeran shugaban kasa a jam’iyyar PDP ya sha alwashin siyar da kamfanin NNPC har idan aka zabe shi a zaben ranar Asabar 23 ga watan Fabrairu .

Amman sanata Akpabio yace yan Niger Delta ba za su yi sha’awan siyar da kamfanin NNPC ba.

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Mutane 5 ne suka mutu a harin da aka kaiwa magoya bayan Kwankwaso

A halin da ake ciki, Legit.ng ta rahoto a baya cewa shugaban jam'iyyar People’s Democratic Party (PDP) na jihar Yobe, Alhaji Sani Inuwa Nguru ya fice daga PDP ya koma jam'iyyar APC.

Nguru ya ziyarci shugaban kasa Muhammadu Buhari a fadar Aso Villa tare da jigo a jam'iyyar APC ma jihar Yobe Mohammed Yahuza.

Tsohon shugaban na PDP ya shaidawa manema labarai cewa ya ziyarci shugaba Muhammadu Buhari ne domin ya jadada mubaya'arsa a gare shi tare da bayyana masa cewa ya komo gida.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel