Yanzu-yanzu: Kotu ta yanke hukunci, APC zata fitar da yan takara a Zamfara

Yanzu-yanzu: Kotu ta yanke hukunci, APC zata fitar da yan takara a Zamfara

Labarin da ke shigo mana da duminsa na nuna cewa wata kotun daukaka kara dake zaune a birnin tarayya Abuja ta yanke sabon hukuncin kan dambarwan fitar da yan takaran jam'iyyar All Progressives Congress APC a jihar Zamfara.

Kotun daukaka karan ta yi watsi da shari'ar babban kotun tarayya da ke Abuja wacce ta halaltawa hukumar gudanar da zabr ta kasa mai zaman kanta INEC hana jam'iyyar APC fitar da yan takara a zaben 2019 da zai gudana a ranan 23 ga watan Febrairu da 9 ga watan Maris, 2019.

An dade ana jeka ka dawo tsakanin hukumar INEC da jam'iyyar APC kan rashin gudanar da zaben fidda gwani kafin ranan INEC ta kulle. Tun lokacin suka dinga safa da marwa a kotuna daban-daban.

KU KARANTA: Shugaba Muhammadu Buhari ya samu gagarumin karuwa, yan takara 12 sun janye masa

A bangare guda, Kotun kolin Najeriya ta yi watsi da karar da jam''iyyar All Progressives Congress APC ta shigar na kalubalantan shari'ar babban kotun jihar Ribas wacce ta haramtawa jam'iyyar gudanar da zaben fidda gwani a shekarar 2018.

Wannan na nuna cewa jam'iyyar APC ba za tayi musharaka a zaben 2019 ba a dukkan kujerun takara a jihar Ribas.

Shugaba Muhammadu Buhari ya nuna bacin ransa ga abinda ya faru da jam'iyyar APC a jihar Ribas amma yace hakan ba babban matsala bane ga jam'iyyar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel