Yanzu Yanzu: Mutane 5 ne suka mutu a harin da aka kaiwa magoya bayan Kwankwaso

Yanzu Yanzu: Mutane 5 ne suka mutu a harin da aka kaiwa magoya bayan Kwankwaso

- An kashe mutane biyar yayinda wasu da dama suka jikkata lokacin da rikicin ya kaure tsakanin mabiyan Kwankwaso da Jibrin Kofa

- Rikicin ya fara ne lokacin da ayarin motocin Sanata Kwankwaso dake dawowa daga gangamin kamfen suka bi ta hanyar inda magoya bayan Kofa ke addu’a don gudanar da zabe cikin kwanciyar hankali da lumana

- Jibrin yace an kona ababen hawa 60 baya ga gidansa

Akalla mutane biyar ne aka rahoto cewa sun mutu a ranar Alhamis, 21 ga watan Fabrairum a yankin karamar hukumar Bebeji da ke jihar Kano yayinda magoya bayan tsohon gwamnan jihar Kano, Sanata Rabi’u Kwankwaso da na tsohon shugaban kwamitin kasafi na majalisar wakilai, Alhaji Abdulmumin Jibrin Kofa suka kara.

Jaridar The Nation ta ruwaito cewa rikicin ya fara ne lokacin da ayarin motocin Sanata Kwankwaso dake dawowa daga gangamin kamfen suka bi ta hanyar inda magoya bayan Kofa ke addu’a don gudanar da zabe cikin kwanciyar hankali da lumana.

Yanzu Yanzu: Mutane 5 ne suka mutu a harin da aka kaiwa Kwankwaso

Yanzu Yanzu: Mutane 5 ne suka mutu a harin da aka kaiwa Kwankwaso
Source: Facebook

Legit.ng ta tattaro cewa ayarin motocin Kwankwaso sun hargitsa taron addu’an, wanda hakan ya haddasa rikici day a kai da zubar jinin da har mutane biyar suka mutu yayinda wasu daga bangarorin biyu suka jikkata.

KU KARANTA KUMA: Zabe: Shugaban PDP na jihar Yobe ya koma APC, ya yi mubaya'a ga Buhari

Da yake tabbatar da lamarin, Kofa ya fada ma jaridar The Nation cewa magoya bayan Sanata Kwankwaso sun kai ma kungiyar hari a hanyarsu ta dawowa Bebeji da Kiru.

A cewarsa an kona ababen hawa 60 baya ga gidansa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel