Zabe: Shugaba Buhari zai taya duk wanda ya yi nasara murna – Kungiyar kamfen

Zabe: Shugaba Buhari zai taya duk wanda ya yi nasara murna – Kungiyar kamfen

- Kungiyar kamfen din dan takarar Shugaban kasa na jam’iyyar APC ta bayyana cewa Buhari zai taya duk wanda yayi nasarar lashe zabe murna

- Kungiyar tace hakan ne zai faru duk da sun san cewa babu makawa Shugaban kasar ne zai lashe zaben mai zuwa

- Ta kuma bayyana cewa Shugaban kasar zai yi godiya ga yan Najeriya bisa goyon bayan da suke bashi da kuma fitowa da suka yi a zaben kasar

Kungiyar kamfen din dan takarar Shugaban kasa na jam’iyyar All Progressives Congress (APC) ta bayyana cewa Shugaban kasa Muhammadu Buhari zai taya duk wanda yayi nasarar lashe zabe murna idan har aka gudanar dashi kan tafarkin na gaskiya da amana.

A cewar kungiyar hakan ne zai faru duk da sun san cewa babu makawa Shugaban kasar ne zai lashe zaben mai zuwa.

Zabe: Shugaba Buhari zai taya duk wanda ya yi nasara murna – Kungiyar kamfen

Zabe: Shugaba Buhari zai taya duk wanda ya yi nasara murna – Kungiyar kamfen
Source: Twitter

Kungiyar kamfen din ta kuma bayyana cewa Shugaban kasar zai yi godiya ga yan Najeriya bisa goyon bayan da suke bashi da kuma fitowa da suka yi a zaben kasar.

Mataimakin darakta janar na kungiyar Waziri Bulama, wanda ya bayyana hakan yace kungiyar tayi gagarumin kamen sannan cewa babu ta yadda za a yi APC ta adi zabe, inda ya kara da cewa yan Najeriya sun yi ammana da Shugaban kasar da kuma APC a wannan zaben.

KU KARANTA KUMA: Jihohi 19 sun kammala jigilar kayan zabe – INEC

A baya Legit.ng ta rahoto cewa a ranar Alhamis 21 ga watan Fabrairu ne shugaban jam'iyyar People’s Democratic Party (PDP) na jihar Yobe, Alhaji Sani Inuwa Nguru ya fice daga PDP ya koma jam'iyyar APC.

Nguru ya ziyarci shugaban kasa Muhammadu Buhari a fadar Aso Villa tare da jigo a jam'iyyar APC ma jihar Yobe Mohammed Yahuza.

Tsohon shugaban na PDP ya shaidawa manema labarai cewa ya ziyarci shugaba Muhammadu Buhari ne domin ya jadada mubaya'arsa a gare shi tare da bayyana masa cewa ya komo gida.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel