Babbar Magana: ‘Yan daba sun kai wa tawagar Osinabjo hari a Ilorin

Babbar Magana: ‘Yan daba sun kai wa tawagar Osinabjo hari a Ilorin

Wasu ‘yan dabar siyasa da ake zargin magoya bayan jam’iyyar PDP ne sun kai wa tawagar mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo, hari a yau, Alhamis, jihar Kwara lokacin da ya je yakin neman zabe.

Rahotannin sun bayyana cewar harin da matasan su ka kai ya saka jami’an tsaro harba bindiga, lamarin da ya kai ga wasu magoya bayan jam’iyyar APC biyu sun samu rauni.

Mutane da yawa sun samu raunuka yayin da su ka tarwatse domin tsira da lafiyar su.

Amma wata majiya daga cikin jami’an ‘yan sanda ya ce harin ya faru ne a unguwar Isale-Koko da ke wajen garin Ilorin bayan ayarin mataimakin shugaban kasar ya wuce.

Da aka tuntubi kakakin rundunar ‘yan sanda na jihar Kwara, Ajayi Okasanmi, ya ce ba zai iya tabbatar da faruwar kai harin ba.

Babbar Magana: ‘Yan daba sun kai wa tawagar Osinabjo hari a Ilorin

Osinabjo
Source: Twitter

Da ya ke Karin haske a kan faruwar lamarin, dan takarar gwamnan jihar Kwara a jam’iyyar APC, Abdulrahman Abdulrazaq, ya yi alla-wadai da harin da harin da ‘yan dabar su ka kai wa tawagar Osinbajo.

DUBA WANNAN: ‘Yan dabar siyasa sun saka wa gidan Abdulmuminu Kofa wuta a Kano, bidiyo

A jawabin da Rafiu Ajakaye, mai taimaka dan takarar gwamnan a bangaren yada labarai ya fitar ya ce, “wasu shaidanun ‘yan dabar siyasa sun kai wa tawagar mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo, hari a yankin Isale Aluko a Ilorin lokacin da yak e gudanar da yakin neman zabe.

“Sun bude wuta a kan tawagar matimakin shugaban kasa a wani salo irin wanda ya faru a lokacin fashin garin Offa."

Dan takarar gewamnan ya yi zargin cewar wasu manyan ‘yan jam’iyyar PDP ne a jihar ke bawa ‘yan dabar muggan makamai domin su yi amfani da su don cimma muguwar manufar su.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel