Nau'ikan shiga 10 da shugaba Buhari ya yi a tsakanin yakin zaben 2015 da 2019

Nau'ikan shiga 10 da shugaba Buhari ya yi a tsakanin yakin zaben 2015 da 2019

- A yayin da ya rage sauran kwanaki kalilan babban zaben kasa ya gudana, ba bu wanda ke da tabbaci ko kuma ta cewa akan yadda sakamakon zaben zai kasance.

- Jam'iyyar APC ta yi nasara a yayin zaben 2015 inda a halin yanzu ta ke ci gaba da jagorancin kasar nan.

- Buhari ya yi basaja daban-daban yayin gudanar da yakin sa na neman zaben a 2015 da kuma bana

Cikin jerin 'yan takarar kujerar shugaban kasa da za su fafata a babban zaben kasa da za a gudanar a ranar Asabar, 23 ga watan Fabrairun 2019, dan takarar jam'iyyar APC, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kasance akan sahu na gaba.

Kazalika shugaban kasa Buhari a karkashin inuwa ta jam'iyyar APC na daya daga cikin 'yan takara da suka kasance akan sahu na gaba wajen fafatawa a yayin babban zaben kasa na shekarar 2015 da ta gabata.

Kasancewa jagoran kasa makamanciyar Najeriya na tattare da nauyi na wakilcin dukkanin kabilun da ta kunsa. Hakan ya sanya shugaban kasa Buhari ya yi basaja tare da bad da kama wajen yin shiga irin ta wasu kabilu daban-daban yayin gudanar da yakin sa na neman zabe a bana da kuma babban zabe da ya gudana a baya.

Masu sharhi akan harkokin siyasa sun bayyana cewa, shugaban kasa Buhari ya yi shiga irin ta wasu kabilu da kasar nan ta kunsa yayin yakin sa na neman zabe da babbar manufa ta isar da sakon sa na hadin kai tamkar tsintsiya madauri daya.

KARANTA KUMA: Jam'iyyar APC reshen jihar Ribas da Zamfara ba za su yi takara ba a zaben 2019 - INEC

Domin tabbatar da shirin sa na kasancewa wakilin dukkanin kabilu da kasar nan ta kunsa, shugaba Buhari ya basajar shiga cikin wasu jihohin kasar nan yayin yakin sa na neman zabe a shekarar 2015 da kuma na bana.

Jaridar Legit.ng ta kawo muku wasu nau'ikan shiga da basajar shugaban kasa Buhari yayin yakin sa na neman zaben a 2015 da kuma bana:

1. Buhari a jihar Legas

2. Buhari a jihar Bauchi

3. Buhari a jihar Benuwe

4. Buhari a jihar Ebonyi

5. Buhari cikin shigar kabilar Ibo

6. Buhari a jihar Cross River

7. Buhari cikin shiga ta Bahaushe

8. Buhari cikin shiga ta Kudu maso Gabashin Najeriya

9. Buhari cikin shiga ta babbar riga

10. Buhari a jihar Abia

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na zaurukan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel