Jihohi 19 sun kammala jigilar kayan zabe – INEC

Jihohi 19 sun kammala jigilar kayan zabe – INEC

Hukumar INEC ta bayyana cewa jihohi 19 sun kammala tura kayan zabe zuwa wuraren da za a gudanar da zabe, yayinda sauran jihohi za su kammala tura nasu a daren Yau Alhamis.

Hukumar har ila yau dai ta bayyana cewa tayi rabe-raben katin zabe miliyan 72.5

Shugaban hukumar INEC, farfesa Mahmood Yakubu, ya bayyana hakan ne a ranar Alhamis yayinda yake bada bayanai akan shirye-shiryen hukumar gabannin zabbukan ranar Asabar.

Jihohi 19 sun kammala jigilar kayan zabe – INEC

Jihohi 19 sun kammala jigilar kayan zabe – INEC
Source: UGC

A cewar shi, “daga cikin mutane miliyan 84 wadanda hukumar tayi wa rijista, an karbi katin zabe miliyan 72.775,502. Katin zabe 11,228,582 suna nan ba tare da an amsa ba.”

KU KARANTA KUMA: Kwararowar kudaden kasashen ketare: Fadar shugaban kasa ta shiga damuwa

Hukumar ta bayyana cewa jihar Legas ce tafi yawan wadanda suka karbi katin zabe, kimanin mutane 5.531389 ne suka karbi latin zabe wanda ya kasance kashi 84.19 ma wadanda suka karbi katin zabe, sannan jihar Kano ce tazo na biyu da katin zabe 4,696747 karbabbu, sannan jihar Bayelsa ce take da mafi kankancin katin zabe guda 769,509 wanda yayi daidai da kashi 83.

Yakubu ya dage da cewa matsayin hukumar akan jam’iyyar All Progressives Congress (APC) a jihohin Zamfara da Rivers bata canja ba.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel