An bindige har lahira, wani masoyin Buhari a Birnin Nsukka

An bindige har lahira, wani masoyin Buhari a Birnin Nsukka

- Tashin hankali ya mamaye gundumar Eha Alumona dake karamar hukumar Nsukka sakamakon kashe dan gani kashenin APC da akayi

- Ishienyi saurayi mai shekaru 24 an bindige shine bayan ya dawo daga taron da PDP ta gayyace shi

- Hukumar 'yan sandan yankin tace bata san da kisan ba kuma bazata bincika ba

An bindige har lahira, wani masoyin Buhari a Enugu

An bindige har lahira, wani masoyin Buhari a Enugu
Source: UGC

Tashin hankali ya samu Eha Alumona, karamar hukumar Nsukka dake jihar Enugu sakamakon harbe dan gani kashenin jam'iyyar APC, Mr Chukwuemeka Ishienyi da aka yi a ranar laraba.

An harbe mamacin ne yayin dawowa daga taron da ake zargi PDP ta shirya a gudumar Eha Uno dake Nsukka.

Ishienyi mai shekaru 24, da namiji daya tal ga mahaifiyar shi kamar yanda wakilin ofishin dillancin labarai ya sanar. Saurayin babban mai goyon baya ne ga PDP kafin ya shiga ayarin samari 100 da suka koma APC a watan da ya gabata.

Amma kuma jami'in hulda da jama'a na hukumar yan sandan jihar Enugu, DSP Ebere Amaraizu, yace ba a sanar dashi aukuwar lamarin ba kuma "ba zan bincika ba".

Amma shugaban APC na gundumar Eha Uno, Mr Lawrence Alumona, ya sanar da manema labarai yanda Ishienyi da abokan shi suka zo suke sanar dashi sun gaji da PDP kuma suna son komawa APC.

Kamar yanda shugaban ya fada, tun bayan da mamacin ya koma APC yake samun barazanar mutuwa.

GA WANNAN: Sakataren PDP na jihar Uzor Kalu ya ajje aikinsa ana tsaka da tsare-tsaren cin zabe

Alumona yace a ranar da Ishienyi ya mutu, ya sanar dashi cewa PDP sun gayyace shi taro, taron da bai dawo da ranshi ba kenan.

Wani mai goyon bayan APC a yankin, Mr Okwudili Ugwu, yace a yammacin ranar da mamacin ya rasu, yana tare dashi dashi har karfe 8 na dare. Kawai sai ji yayi ya rasu da safiyar laraba.

Ugwu yace matasan da suka kai gawar shi asibiti suna rera waka mai nuna karya doka. Yace gawar tana asibitin Umuabor.

Tsohuwar kakar wanda aka kashen, Mrs Veronica Ishienyi ta bada labarin yanda mummunan labarin ya iske ta.

"A ranar laraba da safe, wasu yan cocinmu sun zo suke tambayata dalilin da yasa banje coci da safe ba. Na sanar dasu cewa ina ciwon kafa shiyasa banje ba. Bayan dan wani lokaci ba tare da boye boye ba suka fada min Chukwuemeka ya rasu. Na tambaye su wanne, sai suka ce jikana. Nayi kuka sosai amma nasan hakan ba zai dawo dashi ba. A halin yanzu gawar shi tana asibiti," inji kakar shi.

Yayar shi Ifeanyi da tazo daga Enugu tace ta girgiza da jin labarin mutuwar kaninta daya tak a duniya.

"Da farko cemin akayi hatsari yayi, daga baya ne na gano cewa harbe shi akayi," tace bata san ma yana siyasa kamar hakan ba.

Amma kuma shugaban PDP na gundumar Eha Uno, Austin Odo yace bai kira Chukwuemeka wani taro ba. Yace akwai tarukan jam'iyyar kala kala da akeyi, zai yuwu yaje daya daga ciki ne kafin mutuwar shi.

Shafin NAIJ.com Hausa ne ya koma LEGIT.ng Hausa

Latsa kuga sabuwar manhajar Legit.ng Hausa a wayarku ta salula: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafukanmu na dandalin sada zumunta sune:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel