Olu Falae, ya rattaba takardar ajje aiki daga shugabantar SDP

Olu Falae, ya rattaba takardar ajje aiki daga shugabantar SDP

- Ciyaman na jam'iyar SDP ya mikawa hukumar zabe takaddar barinshi aiki

- Ya rubuta takaddar ne a ranar 19 ga watan Fabrairu inda ta isa wajen ciyaman na hukumar zabe a ranar Alhamis

- Kafin zuwan wannan lokaci ciyaman din zaibar kan kujerar tasa ne a watan Mayu shekara ta 2020

Olu Falae, ya rattaba takardar ajje aiki daga shugabantar SDP

Olu Falae, ya rattaba takardar ajje aiki daga shugabantar SDP
Source: Depositphotos

Tsohon sakataren gwamnati kuma dan takarar shugabancin kasa a jam'iyar Alliance for Democracy a zaben shekara ta 1999 Chief Olu Falae ya mikawa ciyaman din hukumar zabe ta kasa (INEC) Prof Mahmood Yakubu tahardar barin shi aiki.

Takaddar barin aikin wadda aka rubuta ta tun a 19 ga watan Fabrairu ta samu isa wajen ciyaman na hukumar zaben a ranar Talata ta hannun daraktan SDP Hon Yemi Akinbode.

Falae yace deputy national chairman na yankin sa Prof Tunde Adeniran zai cigaba da aiki a matsayin sa na National chairman har zuwa lokacin da wa'adin sa zai kare a watan Mayu shekara ta 2020.

GA WANNAN: Sakataren PDP na jihar Uzor Kalu ya ajje aikinsa ana tsaka da tsare-tsaren cin zabe

Takaddar tana dauke da bayani kamar haka:

"Ina farin cikin bayyana maka cewa na ajjiye aiki na a matsayin ciyaman na SDP tun daga 8 ga watan Fabrairu shekara ta 2019,sannan bisa ga dokokin jam'iyar tamu section 13.2(2) Prof Tunde Akindole sai hau kujera ta har zuwa lokacin da wa'adi na zai cika a watan Mayu shekara ta 2020".

"Ina mika godiya ta a gareka,kwamishinonin ka da sauran abokan aiki bisa kyautatawar su a gareni a lokacin da nake matsayin ciyaman na SDP".

Shafin NAIJ.com Hausa ne ya koma LEGIT.ng Hausa

Latsa kuga sabuwar manhajar Legit.ng Hausa a wayarku ta salula: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafukanmu na dandalin sada zumunta sune:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel