Jam'iyyar APC reshen jihar Ribas da Zamfara ba za su yi takara ba a zaben 2019 - INEC

Jam'iyyar APC reshen jihar Ribas da Zamfara ba za su yi takara ba a zaben 2019 - INEC

Da sanadin shafin jaridar The Punch mun samu cewa, hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta wato INEC, ta cimma matsayar karshe kan hukunci na haramcin takarar jam'iyyar APC reshen jihar Ribas da Zamfara a zaben 2019.

A yayin da rage saura kwanaki biyu kacal a gudanar da babban zabe, hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta ta bayyana cewa, hukunci na haramcin tsayar da 'yan takara na jam'iyyar APC reshen jihar Zamfara da kuma Ribas na nan daram.

Shugaban hukumar INEC; Farfesa Mahmood Yakubu

Shugaban hukumar INEC; Farfesa Mahmood Yakubu
Source: Twitter

Shugaban hukumar INEC, Farfesa Mahmood Yakubu, shine ya bayyana hakan cikin wata hira a jiya Laraba yayin ganawar sa da manema labarai cikin babban birnin kasar nan na tarayya kamar yadda majiyar jaridar Legit.ng ta ruwaito.

Hukuncin Farfesa Yakubu bai sauya ba biyo bayan wata rubutacciyar wasika da Lauyan kolu na Najeriya, Abubakar Malami ya aike da ita domin neman hukumar INEC ta amince da takarar jam'iyyar APC reshen jihar Zamfara.

Rahotanni sun bayyana cewa, jam'iyyar APC reshen jihohin biyu da ke ci gaba da fuskantar wannan dambarwa ta rashin samun damar tsayar da 'yan takara sun yi barazanar haramta gudanar da duk wani zabe a cikin jihohin.

KARANTA KUMA: Kai tsaye za mu bayar da aiki ga masu yiwa kasa hidima da suka yi kwazo yayin aikin zaben 2019 - Farfesa Yakubu

Jaridar Legit.ng ta fahimci cewa, yayin da babban zaben kujerar shugaban kasa ya rage saura kwanaki biyu kacal, jam'iyyar APC reshen jihohin biyu ba za ta yi takara ba a zabukan 'yan majalisun tarayya da kuma na gwamnoni gami da na 'yan majalisun dokoki na jiha.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na zaurukan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel