Dalla-dalla: INEC ta yi bayanin yadda za ta biya ma’aikatan wucin gadi

Dalla-dalla: INEC ta yi bayanin yadda za ta biya ma’aikatan wucin gadi

Hukumar zabe mai zaman kan ta (INEC) ta ce babu banbanci tsakanin matasa ma su bautar kasa (NYSC) a tsarin biyan kudin aikin wucin gadi da za su yi wa hukumar yayin zabukan shekarar nan.

Da ya ke Magana da ma su ruwa da tsaki a Abuja ranar Laraba, shugaban INEC, Farfesa Mahmood Yakubu, ya ce hukumar ba za ta nuna banbanci a biyan alawus din 30,500 a tsakanin ma’aikatan wucin gadi ba.

Duk wanda ya yi aiki na wucin gadi a ranar zabe za a biya shi kudin mota N9,000, na abinci N4,000 wanda idan aka hada zai zama N13,000 a kowanne zabe. Za mu biya N17,500 a zaben shugaban kasa. A zabe na biyu kuma za mu biya N13,000 tunda ba horo za a sake bawa ma’aikata ba, idan aka hada jimilla zai bayar da N30,500. Wannan shine kudin da za mu biya matasa ‘yan bautar kasa,” a cewar Farfesa Yakubu.

Farfesa Yakubu ya bayyana cewar hukumar INEC za ta bayar da aiki kyauta ga matsa ‘yan bautar kasa da su ka yi aiki bisa tsari da ka’ida.

Dalla-dalla: INEC ta yi bayanin yadda za ta biya ma’aikatan wucin gadi

Shugaban hukumar INEC; Farfesa Mahmood Yakubu
Source: Twitter

Shugaban na INEC ya yi wannan alkawari ne domin karfafa wa matasan gwuiwa don kar su bari a yi amfani da su wajen aikata magudin zabe.

Ko a yau, Alhamis, sai da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana mamaki da damuwar sa a kan adadin makudan kudaden kasashen ketare da ke kwararo wa cikin kasar nan domin yin amfani da su wajen sayen kuri’un ma su zabe ranar Asabar.

DUBA WANNAN: Kwararowar kudaden kasashen ketare: Fadar shugaban kasa ta shiga damuwa

Malam Garba Shehu, babban mai taimaka wa shugaba Buhari a bangaren yada labarai, ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar yau, Alhamis, a Abuja. Ya ce shugaba Buhari ya nuna damuwar sa yayin zaman majalisar zartar (FEC) da aka yi jiya, Laraba.

Shugaba Buhari ya zargi wasu ‘yan siyasa da karya dokokin safarar kudi saboda mayatar su ta son ganin sun samu mulki ta kowanne hali.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel