Zabe: Za a yaudari ma su zabe da jabun daloli - EFCC

Zabe: Za a yaudari ma su zabe da jabun daloli - EFCC

Hukumar yaki da cin hanci da rashawa (EFCC) ta yi gargadin cewa akwai dalolin jabu da ke yawo a adin kasar.

Hukumar ta fitar da gargadin ne bayan bayanan sirri da ta samu a lokacin da ake shirin zaben shugaban kasa da na 'yan majalisar tarayya a ranar 23 ga watan abrairu.

Har ila yau hukumar ta EFCC ta yi kira ga 'yan canji da su yi taka-tsantsan.

Zabe: Za a yaudari ma su zabe da jabun daloli - EFCC

Zabe: Za a yaudari ma su zabe da jabun daloli - EFCC
Source: Depositphotos

Sanarwar da EFCC ta fitar ta ce akwai dalolin da suka yi kama da na kwarai amma kuma binciken hukumar ya tabbatar da jabu ne.

Hukumar ta bukaci 'yan canji su sa ido sosai har zuwa a kammala zabe.

KU KARANTA KUMA: Yan Najeriya zan saida wa NNPC ba abokai na ba - Atiku

A wani lamari makamancin haka Legit.ng ta rahoto cewa Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana mamaki da damuwar sa a kan adadin makudan kudaden kasashen ketare da ke kwararo wa cikin kasar nan domin yin amfani da su wajen sayen kuri’un ma su zabe ranar Asabar.

Buhari ya nuna damuwar sa yayin zaman majalisar zartar (FEC) da aka yi jiya, Laraba. Shugaba Buhari ya zargi wasu ‘yan siyasa da karya dokokin safarar kudi saboda mayatar su ta son ganin sun samu mulki ta kowanne hali.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel