Zabe: Shugaban PDP na jihar Yobe ya koma APC, ya yi mubaya'a ga Buhari

Zabe: Shugaban PDP na jihar Yobe ya koma APC, ya yi mubaya'a ga Buhari

A yau Alhamis 21 ga watan Fabrairu ne shugaban jam'iyyar People’s Democratic Party (PDP) na jihar Yobe, Alhaji Sani Inuwa Nguru ya fice daga PDP ya koma jam'iyyar APC.

Nguru ya ziyarci shugaban kasa Muhammadu Buhari a fadar Aso Villa tare da jigo a jam'iyyar APC ma jihar Yobe Mohammed Yahuza.

Tsohon shugaban na PDP ya shaidawa manema labarai cewa ya ziyarci shugaba Muhammadu Buhari ne domin ya jadada mubaya'arsa a gare shi tare da bayyana masa cewa ya komo gida.

DUBA WANNAN: Jajiberin zabe: Wani shiri da Atiku ya kulla da jam'iyyu 5 ya samu matsala

Da dumi-dumi: Shugaban PDP ya koma APC a jihar Yobe

Da dumi-dumi: Shugaban PDP ya koma APC a jihar Yobe
Source: Twitter

Shine shugaban jam'iyyar APC na farko a jihar bayan anyi maja a jihar inda ya kara da cewa duk wani mamba na jam'iyyar ANPP da CPC masoyin shugaba Muhammadu Buhari ne.

Nguru ya sanar da komawarsa jam'iyyar APC ne kasa da sa'o'i 40 gabanin babban zaben shugabancin kasa da za a gudanar a ranar Asabar 23 ga watan Fabrairun 2019.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel