Babu maganar dage da zaben Shugaban kasa a karshen makon nan – INEC

Babu maganar dage da zaben Shugaban kasa a karshen makon nan – INEC

Shugaban hukumar zabe mai zaman kan-ta watau INEC na kasa, Farfesa Mahmood Yakubu, ya bayyana cewa babu abin da zai sa a dakatar da zaben shugaban kasa da aka shirya sai da ikon a Ubangiji.

Babu maganar dage da zaben Shugaban kasa a karshen makon nan – INEC

Sha’anin Ubangiji kurum zai sa a dage zaben bana kuma- INEC
Source: Facebook

Farfesa Mahmood Yakubu ya bayyana cewa zabin Allah na lamarin Ubangiji ne kurum zai sa INEC ta dage zaben da aka tsara za ayi a Ranar Asabar mai zuwa. Kamar yadda mu ka ji, Yakubu ya bayyana wannan ne cikin makon nan a Abuja.

Shugaban hukumar INEC na kasa ya fadawa bakin kasar wajen da su ka shigo Najeriya domin lura da harkar zabe cewa babu abin da zai sa a gaza gudanar da zaben shugaban kasa da na ‘yan majalisan tarayya a Ranar Asabar mai zuwa.

Wani babban kwamishinan hukumar INEC na kasa, Dr. Mustapha Lecky, shi ne ya wakilci shugaban hukumar a wajen wannan taro da ma’aikatar harkokin gida na Najeriya ta shirya a babban birnin tarayya Abuja a cikin wannan makon.

KU KARANTA: Sarki Kano Sanusi II ya bayyanawa jama'a wanda za su zaba

Jami’in zaben yake cewa bai ga abin da zai hana ayi zabe a ranar da aka shirya ba, domin kuwa hukumar ta kammala duk wani tanadi na jigilar kayan aikin zabe. Wakilin shugaban hukumar yace ba a fatan abubuwa su jagalgwale.

Babban ma’aikacin hukumar na INEC ya tabbatar da cewa kayan zabe sun isa jihohin kasar, kuma an tabbatar da cewa abubuwa su na tafiya yadda ya kamata. Yanzu dai har wakilan jam’iyyu sun tabbatar da wannan lamari inji hukumar.

Hukumar zaben ta daura laifin matsalar da aka samu a makon da ya gabata a kan jam’iyyun siyasa, inda aka rika kai ruwa rana a kotu a dalilin zabukan fitar da gwani da aka yi kwanaki. INEC tace wannan ya hana a buga takardun zabe da wuri.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Legit

Mailfire view pixel