Zabe: 'Yan bindiga sun kai wa 'yan sanda hari, sun yi awon gaba da bindigu

Zabe: 'Yan bindiga sun kai wa 'yan sanda hari, sun yi awon gaba da bindigu

Wasu 'yan bindiga sun kaiwa 'yan sanda farmaki a garin Yenagoa na jihar Bayelsa inda suka yiwa wani saja rauni kuma suka kwace bindigu biyu kirar AK 47 gabanin babban zabe da za a gudanar a ranar Asabar.

A cewar The Nation, 'yan bindigan sun kai harin ne bayan sojoji sun harbe wani matashi mai shekaru 27 da aka samu da laifin kwacewa abokin aikinsu wayar salularsa a bayan ya yi masa barazana da bindiga a Biogbolo a Yenagoa.

Wata majiyar hukumomin tsaro ta ce 'ayn bindigan sun kaiwa 'yan sanda hari a shigen da suka kafa a sananiyar Berger Junction.

Zabe: 'Yan bindiga sun kai wa 'yan sanda hari, sun yi awon gaba da bindigu

Zabe: 'Yan bindiga sun kai wa 'yan sanda hari, sun yi awon gaba da bindigu
Source: UGC

DUBA WANNAN: Jajiberin zabe: Wani shiri da Atiku ya kulla da jam'iyyu 5 ya samu matsala

'Yan sandan da aka ce sun saba karbar na goro hannun masu ababen hawa ba suyi tsamanin za a kawo musu irin wannan harin ba.

Wadanda suka kai harin sun sace bindigu kirar AK 47 guda biyu bayan sun yiwa wani jami'an dan sanda mai mukamin saja da ya yi kokarin taka musu birki.

Wasu mazauna unguwar sun ce wasu sojoji kai farmaki unguwanin su cikin fushi inda suka rika bude musu wuta babu dalili a Biogbolo.

Lamarin ya janyo zanga-zanga inda wasu mazauna unguwar rufe wasu sassan Mbiama-Yenagoa.

Wani mazaunin unguwar mai suna Bright da ake yiwa lakabi da Albino ya ce: "Muna zaune muna hutuwa ne kwatsam sai sojoji suka far mana kuma kafin mu tambaya abinda ke faruwa sai suka fara harbe-harbe."

A yayin da aka tuntunbe shi, Kakakin 'yan sandan jihar Buswat Asinim, ya ce har yanzu bai samu bayani a kan afkuwar lamarin.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel