Kai tsaye za mu bayar da aiki ga masu yiwa kasa hidima da suka yi kwazo yayin aikin zaben 2019 - Farfesa Yakubu

Kai tsaye za mu bayar da aiki ga masu yiwa kasa hidima da suka yi kwazo yayin aikin zaben 2019 - Farfesa Yakubu

Farfesa Mahmood Yakubu, shugaban hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta wato INEC, ya yi karin haske dangane da goma da ta arziki da hukumar sa za ta yiwa dukkanin masu yiwa kasa hidima da suka yi kwazo yayin aiwatar da aikin zaben 2019.

Farfesa Yakubu ya sha alwashin cewa, hukumar INEC za ta bayar da aiki kai tsaye ga dukkanin masu bautar kasa da suka yi aiki tukuru tare da kwazon gaske yayin aiwatar ayyukan babban zaben kasar nan da za a gudanar a watan Fabrairu da kuma na Maris.

Kai tsaye za mu bayar da aiki ga masu yiwa kasa hidima da suka yi kwazo yayin aikin zaben 2019 - Farfesa Yakubu

Kai tsaye za mu bayar da aiki ga masu yiwa kasa hidima da suka yi kwazo yayin aikin zaben 2019 - Farfesa Yakubu
Source: Twitter

Cikin jawaban karin haske na kullum a jiya Laraba yayin ganawa da masu ruwa da tsaki akan harkokin zaben kasar nan, Farfesa Yakubu ya ce hukumar INEC za ta yi kyakkyawan sakamako akan duk wani kwazo da aka aiwatar yayin gudanar da ayyukan zabe.

Da ya ke ci gaba da jaddada matsayar sa a cikin garin Abuja, Farfesa Yakubu ya ce hukumar INEC ta hada gwiwa da dukkanin hukumomin tsaro wajen bayar da kariya ga masu bautar kasa a fadin kasar nan yayin aiwatar da ayyukan zabe.

KARANTA KUMA: Ba saboda dalilai na siyasa na yi ritaya ba - Sani Kukasheka

Yayin martanin sa dangane da tasgaro da masu bautar kasa suka fuskanta gabani da kuma bayan dage babban zaben kasar nan a makon da ya gabata, Farfesa Yakubu cikin kokarin sa na share masu hawaye ya sha alwashin bayar da aikin yi kai tsaye ga kowanen su da ya yi kwazon gaske wajen gudanar da aiki a babban zaben kasa.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na zaurukan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit

Mailfire view pixel