Ban ga dalilin da zai sa na yi tunanin yin murabus ba - Shugaban INEC

Ban ga dalilin da zai sa na yi tunanin yin murabus ba - Shugaban INEC

Shugaban Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta INEC, Farfesa Mahmood Yakubu ya ce baya fuskantar matsin lamba kuma baya tunanin yin murabus daga aikinsa duk da cewa wasu da dama sun rika kiraye-kirayen cewa ya yi murabus.

Farfesa Yakubu ya yi wannan furucin ne a yau Alhamis a wurin taron manema labarai da aka gudanar a babban birnin tarayya, Abuja.

Ya ce, "Ban ga wani dalilin da zai sanya inyi tunanin yin murabus ba."

Ba bu wani dalilin da zai sanya ni tunanin murabus - shuganban INEC

Ba bu wani dalilin da zai sanya ni tunanin murabus - shuganban INEC
Source: Twitter

DUBA WANNAN: Harbe masu satar akwatin zabe: An samu sabanin ra'ayi tsakanin Buhari da INEC

Shugaban na INEC ya ce har yanzu shine Jagoran shugabanin Zabe na kasa kuma ya kara da cewa ya yi imanin cewa za a gudanar da zabe cikin nasara a watan Fabrairu da Maris.

"Bana fuskantar wata matsin lamba a halin yanzu da muke magana, Ni ne shugaban Hukumar Zabe Mai Zaman kanta INEC ta Najeriya kuma kamar yadda kundin tsarin mulki ya tanada nine shugaban Zabe kuma babban baturen Zabe na zaben shugaban kasa."

Farfesa Yakubu ya ce har yanzu mukaminsa ba ta canja ba saboda haka zai cigaba da gudanar da ayyukansa bisa ikon da kundin tsarin mulkin kasa ta bashi.

Ya kara da cewa babu wani dalilin da zai sanya ya yi tunanin murabus.

Shugaban na INEC ya bayar da tabbacin cewa ba za a sake dage zabe ba. Ya ce hukumar ta mayar da hankali domin sauke nauyin da kudin tsarin mulkin kasa ya dora mata.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel