Kwararowar kudaden kasashen ketare: Fadar shugaban kasa ta shiga damuwa

Kwararowar kudaden kasashen ketare: Fadar shugaban kasa ta shiga damuwa

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana mamaki da damuwar sa a kan adadin makudan kudaden kasashen ketare da ke kwararo wa cikin kasar nan domin yin amfani da su wajen sayen kuri’un ma su zabe ranar Asabar.

Malam Garba Shehu, babban mai taimaka wa shugaba Buhari a bangaren yada labarai, ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar yau, Alhamis, a Abuja. Ya ce shugaba Buhari ya nuna damuwar sa yayin zaman majalisar zartar (FEC) da aka yi jiya, Laraba.

Shugaba Buhari ya zargi wasu ‘yan siyasa da karya dokokin safarar kudi saboda mayatar su ta son ganin sun samu mulki ta kowanne hali.

Kazalika, ya yaba wa kokarin hukumar yaki da cin hanci da karya tattalin arziki (EFCC) bisa nasarar da ta samu na gano wasu makudan miliyoyin dalar Amurka na irin kudaden da aka shigo da su.

Kwararowar kudaden kasashen ketare: Fadar shugaban kasa ta shiga damuwa

Buhari
Source: UGC

Bayan ya jaddada aniyar gwamnatinsa na yaki da duk wani nau’i na cin hanci da karya dokokin safarar kudi, shugaba Buhari ya bukaci ‘yan Najeriya, musamman ‘yan siyasa, da su saka kishin kasa a ran su a yayin da su ka fita domin kada kuria a zabukan da za a yi.

A nata bangaren, jam’iyyar APC ta ce jita-jitar da ake yada wa a kan dalar Amurka miliyan uku da jam’iyyar PDP ke shirin kashe wa a kowacce jiha lokacin zabe abin damuwa ne.

DUBA WANNAN: Atiku ya lissafa jihohin arewa 3 da ake shirin sake daga zabe

Sakataren yada labaran jam’iyyar, Mallam Lanre Issa-Onilu, ne ya bayyana hakan a cikin wani jawabi da ya aike ga manema labarai a Abuja.

Issa-Onilu ya ce yin hakan ya kara tabbatar da cewar idon jam’iyyar PDP ya rufe wajen ganin ta samu mulki ta kowacce hanya. Kazalila ya zargi jam’iyyar da yunkurin sayen ma su zabe bayan sun fada wa duniya da kan su cewar sun a da karfi ne a yanki biyu cikin shida da ake da su a Najeriya.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel