Oshiomhole ya gana da shugabanin APC, ya yi magana a kan magudin zabe

Oshiomhole ya gana da shugabanin APC, ya yi magana a kan magudin zabe

Shugaban jam'iyyar APC na kasa, Adams Oshiomhole ya ce jam'iyyar ba za ta amince da bangan siyasa ba da satar akwatin zabe yayin gudanar da babban zaben kasa na shekarar 2019.

Oshiomhole ya bayyana hakan ne a ranar Alhamis a garin Benin yayin da ya ke zantawa da manema labarai bayan ganawar sirri da ya yi da shugabanin jam'iyyar APC daga kananan hukumomi 18 na jihae Edo.

Ya kuma ce jam'iyyar ba ta da shirin gudanar da magudin zabe.

Oshiomhole ya gana da shugabanin APC, ya yi magana a kan magudin zabe
Oshiomhole ya gana da shugabanin APC, ya yi magana a kan magudin zabe
Source: Facebook

DUBA WANNAN: Sakon Atiku: Ku canja shugaba mai ci kamar yadda ku ka taba yi

"Munyi taro na musamman: Mun hadu a matsayinmu na 'yan gida daya domin saka tabattar da cewa munyi abin da ya dace a matsayin mu na shugabanni domin janyo hankalin mutane su zabi shugaba Muhammadu Buhari.

"A jihar Edo, mun saba kowane mutum kuri'a daya ya ke kadawa, soboda haka ba za mu amince da bangar siyasa ba da satar akwatin zabe," inji shi.

Mr Oshiomhole ya ce shugaba Muhammadu Buhari ya nuna wa al'umma cewa shi mutum ne mai gaskiya da rikon amana saboda haka ya dace a bashi wata damar domin ya karasa ayyukan da ya fara.

"Munyi alkawarin bawa Buhari wani damar karo na biyu saboda irin ayyukan da ya yi karkashin gwamnatin APC a jihar Edo, nayi imanin Buhari zai lashe zabe," inji shi.

A jawabinsa, Gwamna Godwin Obaseki ne jihar Edo ya ve gwamnatinsa ta samu nasarori masu yawa cikin kankanin lokaci saboda goyon bayan da ya ke samu daga shugaban kasa.

"Edo jihar APC ne babu wani tantama a akan hakan.

"Gwamnatin Buhari ta dade tana bamu goyon baya tare da biya mana dukkan bukatunmu; ya kuma mana alkawarin zai kara a kan abinda ya yi a baya," inji Gwamnan.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel