Sarki Muhammadu Sanusi yayi kira ga Mutane game da harkar siyasa

Sarki Muhammadu Sanusi yayi kira ga Mutane game da harkar siyasa

Wani sako ya zo mana inda aka ji Mai Martaba Sarkin Kano yana magana game da harkar shugabancin a musulunci. Sarkin ya gargadi jama’an kasar nan da su daina zaben wadanda ba su cancanta da jagoraci ba.

Sarki Muhammadu Sanusi yayi kira ga Mutane game da harkar siyasa

Sarki Sanusi II yayi kira ga jama'a su zabi kwararru masu amana
Source: Depositphotos

Sarkin Kano yayi kira da a rika zaben mutum mai amana wanda zai rike dukiyar jama’a tare da tsare hakkin jinanen su. Mai martaba Muhammadu Sanusi II ya ja kunne game da zaben wadanda ke zubar da jinin al’umma saboda siyasa.

Mai Martaban yake cewa abin da ya rataya a kan Masu sarauta da Malaman addini shi ne su sanar da jama’a game da irin mutumin da Ubangiji yace a damkawa ragamar jagorancin al’umma. Sarkin yace amana da sanin aiki ake bukata.

A jawabin Sarkin, ya kara da cewa yana da wahala a samu wanda ya hada duka wadannan abubuwa biyu don haka, addini yace jama’a su zabi wanda yake maras gaskiya sosai amma yake da kwarewa a aiki a kan mai amana kurum.

KU KARANTA: Wani ‘Dan Majalisa yayi murabus saboda ya saci Burodi a wani shago

Sarkin na Kano yake cewa mutum mai amana ba zai amfani kowa da amanar sa ba, haka kuma wanda ya san aiki, zai taimaki al’umma a Duniya da ilmin aikin sa, yayin da rashin amanar sa za ta cuce sa lahira bayan ya bar Duniya.

Mai girma Sanusi na biyu yake cewa ana yin siyasa ne domin jama’a su karu a Duniya ba a lahira ba. Sarki ya kuma nemi Malamai da su tsaya a fadawa mutane irin mutumin da za a zaba ba tare da daga hannun kowane ‘dan takara ba.

Tsohon gwamnan na babban bankin Najeriya, CBN, yake cewa shiga fagen tsaida ‘dan takara a Najeriya zai iya jawo ‘yan siyasa da Malamai da Masu sarauta su sabu sabani har a rika maidawa juna maganganu a dalilin kujerar siyasa.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Legit

Mailfire view pixel