Yan kwanaki kafin zabe, manoman shinkafa a Katsina sun mara wa Buhari baya

Yan kwanaki kafin zabe, manoman shinkafa a Katsina sun mara wa Buhari baya

Kungiyar manoman shinkafa na Najeriya wato Rice Farmers Association of Nigeria (RIFAN), reshen jihar Katsina, ta bada umurni ga mambobinta da su zabi shugaban kasa Muhammadu Buhari da Gwamna Aminu Masari a zabe ma zuwa.

Kamfanin dillancin labarai (NAN) ta rahoto cewa, Alhaji Shuaibu Wakili, shugaban kungiyar reshen jihar, ya bayyana hakan a wani jawabi da ya gabatar a Daura a ranar Alhamis, 21 ga watan Fabrairu. Yace kungiyar ta ba da umurnin ne a karshen taronta a Katsina a ranar Laraba.

Wakili ya bayyana cewa umurnin ya zama dole akan kungiyar don tabbatar da goyon baya ga Buhari da Masari idan aka yi la’akari da yunkuri da suka yi wajen sauya harkar noma daga 2015.

Yan kwanaki kafin zabe, manoman shinkafa a Katsina sun mara wa Buhari baya

Yan kwanaki kafin zabe, manoman shinkafa a Katsina sun mara wa Buhari baya
Source: UGC

“Dole mu zabi jam’iyyar APC”, a cewar shugaban kungiyar. Ya bayyana cewa gwamnatin da Buhari ke jagora ta hanyoyin wasu shirye-shirye da ta tanadar a harkar noma, ta samar da miliyoyin ayyuka, dogaro ga kai da hanyoyin sarrafa kayan abinci.

Shugaban ya bayyana cewa Najeriya ta maye gurbin kasashen ketare masu shigowa da kaya.

Kungiyar RIFAN ta cigaba da ganin kokarin gwamnatin tarayya akan samar da kayan aikin noma ga manoma ta shirye-shirye da ta tanadar.

A cewar kungiyar, fiye da manoma 250,000 ne suka ci amfanin shirye-shirye a fadin kananan hukumomin dake jihar.

Yace shirye-shiryen sun haifar da dubban “masu arziki” inda yake karfafa cewa an samarwa manoma takin zamani, irin shuka, na’ura masu samar da ruwa ga shuka, magungunan kashe kwari da haki ta hanyar bada su a matsayin bashi.

KU KARANTA KUMA: Yawan kuri’u daga Arewa da Kudu za su tabbatar da nasarar Buhari – Tsohon kakakin majalisar Ekiti

Ya karfafa cewa kungiyar ta ga ya dace da ta hada kai don nuna goyon baya ga kudurin sake neman zaben Buhari, don bashi daman inganta nasarorin gwamnatin.

Wannan ne shawarar da shugabannin kungiyar na kasa da na jiha suka yanke a jihohi 36 da Babban Birnin Tarayya (FCT) a ranar Talata, 19 ga watan Febrairu a Abuja. Shugaban RIFAN, Aminu Goronyo, ya fada cewa kowanne daga cikin mambobinta guda miliyan 12.2 na kungiyan sun sha alwashin marawa shugaban kasa Buhari baya.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel