Zaben 2019: Hukumar yan sanda ta sauya kwamishinoni a Adamawa

Zaben 2019: Hukumar yan sanda ta sauya kwamishinoni a Adamawa

Hedkwatar rundunar tsaro ta sake wani sauyi ga kwamishinonin yan sanda a jihar Adamawa, kasa da mako guda bayan ta yi wasu sauye-sauye.

Sabon kwamishinan da aka sanya ran zai kula da tsaron zabe a jihar shine Audu Madaki.

Mista Madaki zai maye gurbin Muhammad Mukaddas jaridar Premium Times ta ruwaito.

Sai dai rundunar yan sandar bata itar da wani jawabi game da sauyin ba, amma dai shugabannin yan sandan biyu da abun ya shaa sun tabbatar da sauyin.

A yanzu Mista Mukaddas na a hanyarsa ta zuwa jihar Imo, inda zai kula da tsaron zabe, cewarsa a ranar Alhamis.

Zaben 2019: Hukumar yan sanda ta sauya kwamishinoni a Adamawa

Zaben 2019: Hukumar yan sanda ta sauya kwamishinoni a Adamawa
Source: UGC

Sai dai zuwa yanzu ba a gano musabbabin chanje-chanjen ba a yan kwanaki kadan kain zae, koda dai hakan ba sabon abu bane.

KU KARANTA KUMA: Babu wanda zai mani kawanya idan na hau kujerar Shugaban kasa - Atiku

Masana a harkar siyasa na ganin jihar Adamawa za ta kasance filin daga a zaben Shugaban kasa mai zuwa.

Atiku Abubakar, wanda hine babban abokin adawar Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya fito ne daga jihar Adamawa sannan an san shi a matsayin wanda yafi yawan ma’aikata ta makarantarshi da kasuwanci.

Amma Buhari ma ya shahara sosai a jihar, sannan tawagar kamfen dinsa na ganin zai ja jama’a sosai a jihar da ke da masu zabe akalla miliyan biyu.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Legit Nigeria

Tags:
Mailfire view pixel