Mambobin jam’iyyar ADC fiye da 1000 sun koma jam’iyyar PDP a Ogun

Mambobin jam’iyyar ADC fiye da 1000 sun koma jam’iyyar PDP a Ogun

Mambobin jam’iyyar African Democratic Congress (ADC) sama da 1000 sun sauya a yankin karamar hukumar Arewacin Yewa dake jihar Ogun sun kuma sha alwashin yiwa jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) biyayya.

Masu sauya shekar sun samu jagorancin fasto Adetunde Joseph daga yankin Oungbe, Ita-Oba, Iselu a yankin Arewacin Yewa dake jihar Ogun, inda shugabannin jam’iyyar PDP suka karbi bakuncinsu, tare da shugaban jam’iyyan a jihar, Injiniya Adebayo Dayo; Mataimakin dan takaran gwamna, Dr. Reuben Abati da babban darektan kungiyar Aare Remi Bakare, wanda ya jagoranci sauran masu yakin neman zabe zuwa Kauyukan gbogila, Ketu da Ayetoro, duk a karkashin karamar hukumar Arewacin Yewa a jihar Ogun.

Fastor Joseph yace daga shi har sauran jama’a sun yanke shawaran barin jam’iyyar ADC ne saboda basu son su kasance cikin jam’iyyar da ta gaza tsayar da dan takarar Shugaban kasa.

Mambobin jam’iyyar ADC fiye da dari sun koma jam’iyyar PDP a Ogun

Mambobin jam’iyyar ADC fiye da dari sun koma jam’iyyar PDP a Ogun
Source: Twitter

Ya kara da cewa basu son a bar su a baya a lokacin da PDP zata yi murnar nasaranta, wanda Alhaji Atiku Abubakar da sanata Buruji Kashamu ke wakilta.

Yayinda yake gabatar da jawabi ga jama’a, Dayo ya bukaci da su marawa jam’iyyar PDP baya don dawo da martabar jihar. Ya bada tabbacin cewa sanata Kashamu ya kasance a shirye don “Daga darajar jihar Ogun” har idan aka zabe shi.

A jawabinsa, Dr. Abati yace yayi farin ciki akan yanda jama’a masu yawa suka tarbesu, inda ya kara da cewa shi da yan uwansa zasu gudanar da ayyuka, har idan aka zabe su a zaben gwamna da za a gudanar a ranar 9 ga watan Maris, 2019.

KU KARANTA KUMA: Zaben 2019: Jam’iyyun siyasa 13 sun mara wa Dankwanbo baya domin shiga majalisar dattawa

Yace kafin ranar zabensu za a gudanar da zaben shugaban kasa da na yan majalisa a ranar Asabar, 23 ga watan Fabrairu, 2019, ya kuma bukaci mutane dasu zabi jam’iyyar PDP daga sama har kasa.

Ya baiwa mutane tabbacin cewa kananan hukumomi zasu samu yancin samun kudi, inda ya kara da cewa wannan zai inganta cigaba a kananan hukumomi

Yayinda yake gabatar da jawabi ga mutane, Aare Bakare ya bukaci da su yi amfanin da katin zabensu don zabar yan takaran jam’iyyar PDP.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel