Sakon Atiku: Ku canja shugaba mai ci kamar yadda ku ka taba yi

Sakon Atiku: Ku canja shugaba mai ci kamar yadda ku ka taba yi

Dan takarar shugabancin kasa na jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar ya yi kira ga 'yan Najeriya su fito kwansu da kwarkwata a ranar Asabar su kayar da shugaban kasa mai ci, Muhammadu Buhari kamar yadda suka kayar da Shugaba Goodluck Jonathan a ranar 28 ga watan Maris na 2015.

Atiku ya yi wannan furucin ne a cikin sakon da ya fitar a faifan bidiyo a shafinsa na Twitter.

Tsohon mataimakin shugaban kasa ya ce ranar zabe rana ce da dukkan 'yan Najeriya suke da 'yanci iri daya saboda kowa kuri'a daya ya ke da ita.

Ya bukaci 'yan Najeriya suyi zabe a kan kasancewa da cigaba da rayuwarsu kamar yadda ta ke a cikin shekaru hudu da suka gabata ko kuma su nemi sauya rayuwarsu da abin da yafi alheri.

Atiku ya bukaci 'yan Najeriya su fito suyi zabe ko da kuwa ba jam'iyyarsa na PDP za su kada wa kuri'a ba inda ya kara da cewa babu abu mai muni kamar dan kasa ya yi watsi da hakkinsa na zuwa kada kuri'a.

DUBA WANNAN: Wasu na kusa da Buhari za su taimakawa Atiku samun nasara - PDP

"Ya ku 'yan uwa na 'yan Najeriya, kamar yadda kuka sani za a gudanar da zaben shugaban kasa da na 'yan majalisu a ranar Asabar. Ana gudanar da zabe ne domin bawa al'umma damar bayyana ra'ayoyinsu a kan irin mulkin da aka musu a shekaru hudu da suka wuce da kuma wanda zai mulke su a shekaru hudu masu zuwa.

"A ranar 28 ga watan Maris na 2015, mu 'yan Najeriya munyi tafi rumfunan zabe mun canja shugaban kasa da ke kan karagar mulki. Nayi alfahari da hakan sosai a matsayina na dan Najeriya mai kaunar demokradiyya.

"A ranar Asabar mai zuwa, muna da damar sake maimaita hakan. Sako ne a gare ku mai sauki ne: Don Allah ku fito kuyi zabe domin hakan zaiyi tasiri a kan yadda goben mu za ta kasance a matsayin kasa. A ranar zabe kowa daya ya ke saboda ko wace kuri'a daraja daya ta ke da shi.

"Amma idan ba kuyi zabe ba, hakan na nufin kun amince da yadda ake gudanar da mulkin kasar a shekaru hudu da suka wuce. Kuna da ikon kawo canji a Najeriya da katin zaben ku. Zan fito inyi zabe ranar Asabar kuma ina kira gare ku ku fito kuyi zabe ko da ba PDP za ku zaba ba."

Kalli faifan bidiyon a kasa:

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel