Zaben 2019: Jam’iyyun siyasa 13 sun mara wa Dankwanbo baya domin shiga majalisar dattawa

Zaben 2019: Jam’iyyun siyasa 13 sun mara wa Dankwanbo baya domin shiga majalisar dattawa

- Jam’iyyun siyasa 13 a jihar Gombe sun amince da Gwamna Ibrahim Dankwambo a matsayin dan takarar kujerar sanata

- Dankwambo na neman takarar kujerar dan majalisar dattawa ne a karkashin jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) domin ya wakilci yankin Gombe ta Arewa

- A ranar Asabar 23 ga watan Fabrairu ne dai za a gudanar da zaben majalisar dokokin kasa tare da na shugaban kasa

Jam’iyyun siyasa 13 a jihar Gombe sun amince da Gwamna Ibrahim Dankwambo a matsayin dan takarar kujerar sanata a zaben Shugaban kasa da na majalisar dokoki da za a gudanar a ranar Asabar, 23 ga watan Fabrairu.

Dankwambo na neman takarar kujerar dan majalisar dattawa ne a karkashin jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) domin ya wakilci yankin Gombe ta Arewa.

Zaben 2019: Jam’iyyun siyasa 13 sun mara wa Dankwanbo baya domin shiga majalisar dattawa

Zaben 2019: Jam’iyyun siyasa 13 sun mara wa Dankwanbo baya domin shiga majalisar dattawa
Source: Depositphotos

Legit.ng ta tattaro cewa Malam Auwal Ibrahim, kakakin jam’iyyun siyasar ne ya sanar da goyon bayan Dankwambon a wani taron manema labarai a Gombe a ranar Laraba, 20 ga watan Fabrairu.

Sun yi kira ga magoya bayansu da su zabi Dankwambo a matsayin sanata mai wakiltan yankin Gombe ta arewa.

Ya jaro jam’iyyun siyasa wadanda suka hada da All Grassroots Alliance (AGA), Alliance for Social Democratic (ASD), Change Advocacy Party (CAP), Democratic People’s Congress (DPC), Restoration Party of Nigeria (RPN), Mega Party of Nigeria (MPN) Accord Party (AP).

Sauran sun hada da Advance of Democracy (AD), Better Nigeria Progressive Party (BNPP), Democratic Peoples Party (DPP), Hope Democratic Party (HDP), People Progressives Party (PPP) and Advance Peoples Democratic Party (APDA).

A cewarsa Dankwaambo yayi kokari da mutanen jihar, don haka akwai bukatar bashi damar wakitansu a majalisar dattawa.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel