Zaben 2019: Gwamnatin Tarayya za ta rufe iyakokin Najeriya

Zaben 2019: Gwamnatin Tarayya za ta rufe iyakokin Najeriya

Gwamnatin Tarayya ta sanar da cewa za ta rufe dukkan hanyoyin shigowa Najeriya ta kasa daga karfe 12 na ranar Juma'a 22 ga watan Fabrairun 2019 zuwa karfe 12 na ranar Lahadi 24 ga watan Fabrairun 2019.

A cikin sanarwar da ta fito daga Ministan Harkokin Cikin Gida, Laftanant Janar Abdulrahman Dambazau ya ce an dauki matakin ne domin takaita shige da fice a kan iyakokin Najeriya a ranakun zabe.

Zaben 2019: Za a rufe iyakokin Najeriya gobe

Zaben 2019: Za a rufe iyakokin Najeriya gobe
Source: Depositphotos

DUBA WANNAN: Wasu na kusa da Buhari za su taimakawa Atiku samun nasara - PDP

Kamar yadda yake cikin sakon da Kwantrolla Janar na Immigration, Muhammad Babandede ya aike wa The Nation: Ya ce, "Saboda zaben shugaban kasa da za a gudanar a ranar 23 ga watan Fabrairun 2019, Ministan harkokin cikin gida ya bayar da umurnin rufe dukkan iyakokin kasa daga karfe 12 na ranar Juma'a 22 ga watan Fabrairu zuwa 12 ranar Lahadi 24 ga watan Fabrairun 2019.

"Za a dauki wannan mataki ne domin takaita shige da fice a kan iyakokin Najeriya a ranakun zabe. Ana sanar da al'umma su lura wannan umurnin kuma su tabbatar sunyi biyaya ga umurnin."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel