Yanzu-yanzu: Ban yi murabus ba - Osinbajo ya karyata rahotanni

Yanzu-yanzu: Ban yi murabus ba - Osinbajo ya karyata rahotanni

Mataimakin shugaban kasa, Farfesa yemi Osinbajo, ya karyata rahotannin cewa ya yi murabus daga kujerarsa bisa ga wani sabani da ya samu da shugaba Muhammadu Buhari.

An samu jita-jitan cewa mataimakin shugaban kasan ya nuna bacin ransa kan rashin gayyatarsa ganawar da Buhari da jami'an tsaron da gwamnonin Najeriya ranan Talata, 20 ga watan Febrairu.

Tsohon mai magana da yawun tsohon shugaban kasa, Doyin Okupe ya bayyana cewa an hana Osinbajo shiga dakin taron. Okupe ya bayyana hakan ne a shafinsa na Tuwita inda yace:

"Osinbajo yace ba'a sanar da shi kan ganawar ba, kuma lokacinda ya samu labari, an hanashi shiga. Duk da haka an bari gwamnoni su shiga."

Osinajo ya karyata labarin inda ya ce: "Karya kuma labarin bogi na yawo musamman wannan lokaci da yan Najeriya ke kokarin zaben wanda zai shugabancesu a shekaru hudu masu zuwa."

"Ban yi murabus ba. Ina kan aikina na bautan yan Najeriya karkashin jagorancin shugaba Muhammadu Buhari."

KU KARANTA: Dalilin da yasa kasar Iran ke goyon bayan Atiku - SGN

Mun kawo muku rahoton cewa Shugaba Muhammadu Buhari ya gargadi masu shirin tayar da tarzoma a ranan zabe da cewa su nisanci akwatunan zabe ranan Asabar, 23 ga watan Febrairu, 2019.

A wata ganawar gaggawa da jigogin jam'iyyar All Progressives Congress (APC) sukayi ranan Litinin a birnin tarayya Abuja, shugaban kasa ya ce duk wanda ya tayar da rikici musamman ta hanyar daukan akwatin zabe, to a bakin ransa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Newspaper

Tags:
Online view pixel