Bayan Ghana, Italiya ma ta fara koro 'yan Najeriya saboda kananan laifuka daga zuwansu

Bayan Ghana, Italiya ma ta fara koro 'yan Najeriya saboda kananan laifuka daga zuwansu

- Gwamnatin Italy ta dawo da yan Najeriya 17 gida duk da wa'adin Visa dinsu bai cika ba

- An kama su da laifukan da suka sabawa dokar kasar ne da kuma safarar miyagun kwayoyi

- Tuni hukumar Immigration suka dau bayanin su tare da mika macen mai safarar miyagun kwayoyi ga NDLEA

Bayan Ghana, Italiya ma ta fara koro 'yan Najeriya saboda kananan laifuka daga zuwansu

Bayan Ghana, Italiya ma ta fara koro 'yan Najeriya saboda kananan laifuka daga zuwansu
Source: UGC

Gwamnatin kasar Italy ta dawo da yan Najeriya 17 gida sakamakon kama su da laifin safarar miyagun kwayoyi da tayi.

Wadanda aka dawo da, 16 maza sai mace daya sun sauka a filin jirgin Murtala Muhammed dake Legas a ranar talata.

GA WANNAN: Hukumar Kwastam na kan bincike kan harbi da bindiga, bayan sun halbe wani murus

An gano cewa an dawo da mazan 16 ne sakamakon laifukan da sukayi sun sabawa dokar kasar, ita kuma macen saboda safarar miyagun kwayoyi ne.

Majiyar mu tace jami'an hukumar immigration ta kasa ta dau dalla dallar bayanan su inda daga baya aka barsu su karasa cikin kasar.

Macen da aka kama da laifin safarar miyagun kwayoyin ce aka mika ta ta hukumar NDLEA.

A baya ma dai, kasar Ghana, wadda Najeriya ke kora a shekarun 1980s, ta kama, da koro 'yan Najeriya saboda sun yi yawa kuma ana yawan samun masu laifi a cikinsu. Haka ma a Libya, sai da aka bautar da 'yan Najeriya a 2016-2017.

Shafin NAIJ.com Hausa ne ya koma LEGIT.ng Hausa

Latsa kuga sabuwar manhajar Legit.ng Hausa a wayarku ta salula: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafukanmu na dandalin sada zumunta sune:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel